Yanzu: Bayan Kashe Ƴan Sakai 57, Ƴan Bindiga Sun Sake Kashe Sojoji 13, Ƴan Sanda 5 Da Vigilante a Kebbi

Yanzu: Bayan Kashe Ƴan Sakai 57, Ƴan Bindiga Sun Sake Kashe Sojoji 13, Ƴan Sanda 5 Da Vigilante a Kebbi

  • Yan bindiga sun kai hari kauyen Kanya da ke Danko-Wasagu, a jihar Kebbi inda suka kashe jami'an tsaro da dama
  • Mazauna garin da majiya daga jami'an tsaro sun ce an kashe sojoji 13, yan sanda guda biyar da wani dan sakai daya sannan wasu sun jikkata
  • Majiiya daga garin ya ce maharan sun taho ne a kan babura 200, da mutane uku kan kowanne babur suka shafe fiye da awa uku suna artabu da jami'an tsaro

Kebbi - Yan bindiga sun sake kashe jami'an tsaro 19 cikinsu akwai sojoji 13, a jihar Kebbi, a cewar wata majiyar tsaro da mazauna gari a ranar Laraba, rahoton The Punch.

An yi artabun ne a daren ranar Talata a kauyen Kanya da ke Danko-Wasagu, kwana guda bayan an kashe dimbin yan sakai a yankin.

Kara karanta wannan

Kisan Kebbi: 'Yan majalisa sun roki FG ta tura sojojin sama da kasa domin ragargazar 'yan bindiga

Yanzu: Bayan Kashe Ƴan Sakai 57, Ƴan Bindiga Sun Sake Kashe Sojoji 13, Ƴan Sanda 5 Da Vigilante a Kebbi
Yanzu: Bayan Kashe Ƴan Sakai 57, Ƴan Bindiga Sun Sake Kashe Sojoji 13, Ƴan Sanda 5 Da Dan Sakai a Kebbi. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Daruruwan yan bindiga sun afka Kanya, inda suka fafata da sojoji da yan sanda na tsawon awa uku a cewar majiya da kuma mazauna garin.

"Yanzu mutane 19 aka tabbatar da mutuwarsu. Sun hada da sojoji 13, yan sanda biyar da dan vigilante daya, " a cewar majiyar tsaro da baya so a ambaci sunansa, ya shaida wa AFP.

Ya ce wasu jami'an tsaron ciki har da sojoji guda hudu suna kwance a asibiti ana musu magani saboda rauni da suka yi.

"An gwabza fada sosai na tsawon awanni fiye da uku. Yan ta'addan sun yi galaba saboda suna da matukar yawa."

Rundunar sojoji da yan sanda ba su yi tsokaci kan lamarin ba da aka tuntube su har zuwa lokacin wallafa wannan labarin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan sanda sun mutu yayin da motar tawagar ministocin Buhari ta yi hadari

Muna kyautata zaton yan bindigan da suka kashe yan sakia 57 ne suka kawo mana hari, Arzika

Wani mazaunin garin da ya ce sunansa Musa Arzika, wanda shima ya tabbatar da adadin ya ce maharan sun taho ne a kan babura 200, kowanne mutum uku a kai, suka afka wa kauyen.

Ya ce:

"An kai gawarwakin sojojin 13, yan sanda biyar da dan vigilante daya da suka mutu a fadan zuwa Zuru a safiyar yau."
"Muna kyautata zaton yan bindigan da suka kashe yan vigilante ne suka kawo mana harin."

Yan bindiga da miyagu sun dade suna adabar garuruwa a yankin arewa maso yamma da tsakiya na tsawon shekaru, suna kisa, sata da garkuwa da kone-kone.

An yi wa mahaifi da 'ya'yansa 2 kisar gilla a hanyarsu ta dawowa daga gona

A wani labarin, wasu mahara sun kashe wani mahaifi da 'ya'yansa su biyu, a ranar Alhamis a hanyarsu ta koma wa gida daga gona a garin Ore a kan hanyar Ore Egbeba a karamar hukumar Ado, jihar Benue.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi watsi da ikirarin Abdulmalik Tanko cewa ba shi ya kashe Hanifa ba

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa ana ta samun kashe-kashe a wasu garuruwa da ke kewayen Ado da ke da iyaka da jihar Ebonyi inda ake rikicin kan iyaka sannan ake fama da matsalan hari daga makiyaya.

Mazauna garin sun ce wannan mummunan kisar da aka yi wa yan gida daya; Mr Enogu, Chigbo Enogu da Sundaya Enogu, ya jefa mutanen cikin tsoro ta yadda ba su iya fita su yi harkokinsu yadda suka saba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel