Shiga aikin soja: Abubuwa 5 kuke bukata domin shiga aikin sojin Najeriya

Shiga aikin soja: Abubuwa 5 kuke bukata domin shiga aikin sojin Najeriya

  • Rundunar sojojin Najeriya ta fitar da sanarwar daukar sabbin ma'aikata na shekarar 2022/2023
  • An nemi wadanda ke da sha'awar shiga aikin soja su ziyarci shafin rundunar na yanar gizo don cike fom
  • A nan, mun tattaro wasu abubuwa biyar da dole sai me neman aikin ya cike su

A ranar Talata, 8 ga watan Maris ne, rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewar shirinta na daukar ma’aikata na 2022/2023 na gudana a yanzu haka.

An bukaci wadanda ke sha’awar aikin da su ziyarci shafin daukar aiki na rundunar sojin domin ganin yadda za su nemi aikin, Daily trust ta rahoto.

Shiga aikin soja: Abubuwa 5 kuke bukata domin shiga aikin sojin Najeriya
Shiga aikin soja: Abubuwa 5 kuke bukata domin shiga aikin sojin Najeriya Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Idan kana son shiga aiki soja, dole ka cike wadannan abubuwan bukata:

1. Dole ka kasance dan Najeriya sannan ka mallaki katin shaida na dan kasa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

2. Dole ka mallaki akalla kredit 5, ciki harda Ingilishi a jarrabawar WASSCE, GCE, NECO ko NAPTIB a zama da bai wuci biyu ba.

3. Dole mutum ya kasance da lafiyar jiki da na kwakwalwa kuma kada mutum ya yi kasa da mita 1.68 ga maza ko kuma 1.62 ga mata.

4. Dole mutum ya kasance tsakanin shekara 18 da 26.

5. Dole ne a cire fom din da aka cike ta yanar gizo, a sanya hannu akai sannan a zo dashi cibiyar jarrabawa yayin da aka fara tantance wadanda za su shiga aikin

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa

A wani labari na daban, tsohon dan majalisa da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, Sanata Shehu Sani ya shawarci yan Najeriya da ke da sha’awar shiga yakin Ukraine da Rasha amma kuma basu da kudin biza.

Kara karanta wannan

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

Sanata Sani ya bukace su da su koma yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabashin Najeriya domin nuna kwarewarsu.

Ya kuma bayyana cewa wannan bajinta nasu zai yi matukar amfani wajen yaki da Boko Haram da yan fashin daji sannan kuma cewa basa bukatar biyan kudi a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel