Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amaryar Yusuf Buhari tayi

  • Malamin addinin Islama ya yi tsokaci kan yadda amare ke sanya kayan da suka saba addini lokutan bukukuwansau
  • Malamin ya kuma ja wo hankalin Zahra Bayero a gefe guda kan wani shiga da ta yi a bikin wankar amarya na aurenta
  • Malamin ya yi nuni da irin hatsarin dake tattare da irin wannan shiga, yana mai cewa, ya kamata a duba lamarin

Kano - Babban Malamin addinin Islama, Dr Ibrahim Jalo Jalingo, ya yi tsokaci game da shigar da Zahra Bayero; amaryar Yusuf Buhari, yana mai nuna takaicin yadda 'ya'yan musulmai suka baci da shigar nuna tsiraici.

A makon nan wasu hotuna suka watsu a kafafen sada zumunta, wadanda ke nuna Zahra Bayero, budurwar da dan shugaban kasa Buhari zai aura sanye da wasu kaya masu nuna wane bangare na jikinta.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

Wannan shiga da tayi ya jawo cece-kuce, yayin da mutane da dama suka nuna damuwarsu da cewa, wannan shiga bata yi dace da addinin Islama ba, kamar yadda budurwar take musulma.

Wannan fitsara ne: Malami ya yi tsokaci kan shigar da amayar Yusuf Buhari tayi
Bikin Zahra Bayero | Hoto: @fabricblogger, @trendjournalng
Asali: Instagram

Malamai a bangare guda, sun yi tsokaci kan lamarin, inda shahararren malami Dr Ibrahim Jalo Jalingo ya yi tsokaci mai tsoratarwa kan wannan shiga.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Nasihar malamin bata tsaya kan Zahra kadai ba, malamin ya yi kira ne ga dukkan masu irin wannan shiga, yana mai tuna yadda ake samun 'ya'yan manya a kasar nan da irin wannan dabi'a.

A jiya Laraba 4 ga watan Agusta, malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook inda Legit Hausa ta gano yana cewa:

"1. Lalle irin yadda amare 'ya'yan musulmi suke yin shiga ta nuna tsiraici a mahangar Musulunci sannan kuma su dauki hotunansu cikin wannan shiga ta fitsara su watsa wa Duniya, abin takaici ne matuka. Kuma abu ne da zai iya jawo hushin Allah a kan al'ummar Kasa.

Kara karanta wannan

Bera ya yi batan hanya a ofishin NDLEA, ya fada dakin wiwi, abin da ya yi ya ba da mamaki

"2. Lalle mun ga irin wannan fitsara, da saba Shari'ah, a 'yan shekaru kadan da suka wuce daga wata 'yar shugaban kasa, muka kuma sake ganin irinta daga wata 'yar gwamna, ga shi a yau kuma muna ganin ta daga wata 'yar babban sarki!!
"3. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki cewa kada Ya kama mu da laifin da wawayen cikinmu suke aikatawa. Ameen."

Kasaitattun Bidiyoyi da Hotunan 'Bridal Shower' na Zarah Bayero da Yusuf Buhari

Alamu bayyane suke na cewa tuni aka fara shagalin bikin gidan shugaban kasa da na gidan sarautar Bichi.

Tun a ranar Asabar da ta gabata Legit.ng ta fara kawo muku kyawawan hotunan wasan Polon da aka yi a ranar Juma'a da ta gabata na bikin diyar Sarkin Bichi, Gimbiya Zahra Bayero da dan shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari.

A yau kuwa Legit.ng ta tattaro muku tsula-tsulan hotuna da bidiyoyin wankan amarya, wanda a zamanance aka mayar da shi liyafa mai zaman kanta da ake kira da Bridal Shower.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi abin da ya kamata a yi don habaka kudin shigan man fetur a Najeriya

Hotunan wankan amarya na Zahra Bayero sun bar baya da kura

A wani labarin, Ana shirin yin wani gagaruin biki a Najeriya tsakanin iyalan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da na masarautar Bichi da ke jihar Kano.

Dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari, zai angwance da muradin ransa, Zahra Bayero a ranar 21 ga watan Agusta, 2021. Sai dai tuni aka fara shagulgulan biki inda aka yi wankan Amarya.

A hotunan shagalin da shafin northern_hibiscuss ya wallafa a Instagram an gano Amarya Zahra cikin kwaliyya da doguwar riga fara irin ta turawa, sannan amaryar bata yane kanta da kallabi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: