Ka fi Ronaldo: Bidiyon Obasanjo cike da kwarewa yana taka leda ya kayatar da 'yan Najeriya

Ka fi Ronaldo: Bidiyon Obasanjo cike da kwarewa yana taka leda ya kayatar da 'yan Najeriya

  • Duk da shekarunsa 85, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya nuna karfin jikinsa yayin da ya buga wasan kwallon kafa a farfajiyar gidansa
  • Karamin wasan kwallon kafan da tsohon shugaban kasan ya shiga yana da cikin shagulgulan bikin zagayowar ranar haihuwarsa
  • A yayin wallafa bidiyon Obasanjo a filin kwallon, Sanata Dino Melaye ya kwatanta Obasanjo da dan wasan gaba na Arsenal da Super Eagles

Abeokuta, Ogun - Tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya shiga wasan kwallon kafan da aka yi a filin wasa na farfajiyar gidansa da ke Abeokuta a jihar Ogun.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, wasan kwallon kafan yana daga cikin jerin shagulgulan cikan tsohon shugaban kasan shekaru tamanin da biyar.

Ka fi Ronaldo: Bidiyon Obasanjo cike da kwarewa yana taka leda ya kayatar da 'yan Najeriya
Ka fi Ronaldo: Bidiyon Obasanjo cike da kwarewa yana taka leda ya kayatar da 'yan Najeriya. Hoto daga @dinomelaye
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara

Legit.ng ta tattaro cewa, a karamin wasan kwallon kafan, an ga shugaban kasar jamhuriyar Benin mai shekaru 91, Nicephore Soglo, tsohon ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Bayo Ojo da sauran masoyan wasannin motsa jiki.

Ya alakanta karfin jikinsa da baiwar da Allah yayi masa inda aya bukaci tsofaffi da su dage da atisaye, duba lafiyarsu, cin abinci mai nagarta da kuma tattaunawa da jama'a domin samun tsufa mai kyau.

A yayin wallafa bidiyon tsohon shugaban kasan yana taka leda a fili, tsohon sanatan Kogi na yamma, Dino Melaye, ya yi rubutu kamar haka a shafinsa na Instagram:

"Sabo dan wasa dal, dan wasan gaban da Arsenal da Super Eagles ke nema ido rufe kan £100million."

'Yan Najeriya sun yi martani

Rubutun Sanata Dino Melaye na kasan bidiyon ya janyo martani mai yawa daga 'yan Najeriya.

The landlord Room, @thelandlordroom, tsokaci yayi da: "Sabon dan wasan da Arsenal ta siya ne jiya? Tambaye ce nake yi cike da mutuntawa."

Kara karanta wannan

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

Afuye Ayodele, @genesis_mih, yace: "Sabon mai tsaron gida, Baba fa ya fi Maguire,"
@j.oyekanmi, yace: "Ina kaunar Baba Obasanjo... mutum ne da Ubangiji yayi wa baiwa."

Hotunan Buhari ya na tattakin mita 800, Obasanjo ya na kwallo, Jonathan ya na sassarfa

A wani labari na daban, atisaye a yanzu ba wai jijjiga bane har a yi zufa ba. Masana kimiyya sun gano alaka tsakanin lafiyar jiki a bayyane da kuma karfin kwakwalwa. Ana mamakin dalilin da yasa shugabannin duniya ke atisaye duk da yawan ayyukan da ke kansu.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya na yin wasan kwallon doki. Firayim ministan Canada, Justin Trudeau, ya kan yi wasan dambe.

Hakazalika, ba a bar shugabannin Najeriya a baya ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin tattaki, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya na wasan kwallon kafa yayin da Jonathan na yin sassarfa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel