Bikin sauya sheka: Dan majalisar jiha mai ci ga bar PDP, ya koma APC a Gombe

Bikin sauya sheka: Dan majalisar jiha mai ci ga bar PDP, ya koma APC a Gombe

  • Dan majalisa mai wakiltar Nafada ta Kudu a jihar Gombe ya kaura daga PDP ya koma jam'iyyar APC mai mulkin jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC a Gombe ke yawaitar samun masu sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun siyasa
  • 'Yan APC sun bayyana cewa, zuwan dan majalisar APC zai taimaka matuka wajen tabbatar da ci gaban jam'iyyar a zaben 2023

Jihar Gombe - Yayin da 'yan siyasar Gombe ke ci gaba da kaura daga jam'iyyun siyasar da suke zuwa wasu, a yau an tashi da labarin sauya shekar dan majalisa mai wakiltar Nafada ta Kudu, Hon. Adamu A. Musa daga PDP zuwa APC mai mulkin jihar.

A cikin wata wasika da dan majalisar ya rubuta da hannu, kana aka yada a kafar sada zumunta na Facebook, an ga kalaman da ya yi cikin sauki, inda ya ce zamansa a PDP ya kare.

APC ta samu karuwa a jihar Gombe
Bikin sauya sheka: Dan majalisan jiha mai ci ga bar PDP, ya koma APC a Gombe | Hoto: Abdul No Shaking
Asali: Facebook

Abdul No Shaking, daya daga cikin hadiman gwamnan jihar Gombe kan harkokin kafafen yada labarai na zamani, ya yada hoto tare da wasikar barin PDP na Hon. Adamu A Musa.

Wasikar ba ta bayyana wani dalili na barinsa jam'iyyar ba, kana bata bayyana komawarsa APC, sai dai, hadimin gwamnan ya ce tuni dan majalisar ya shigo APC.

Shigowarsa APC alheri ne, zai jawo mana jama'a

Da Legit.ng Hausa ta tuntubi wani mamban jam'iyyar APC kuma mai sharhi kan siyasa a jihar, Shamsudeen Sani, ya ce duba da gogewar Hon. Adamu Musa jam'iyyar APC, zai zama alheri ga APC.

A cewarsa:

"Wannan ba karamin ci gaba bane ga jam'iyyar APC, domin shigowarsa alheri ne, kuma zai jawo kuri'u a zabe mai zuwa kasancewarsa shugaba da yake da mabiya da yawa."

Hakazalika, ya yi gargadi ga masu shigowa jam'iyyar domin bata ta, inda yace:

"Abu ne sananne, mutane da dama suna shigowa APC, kuma ba wasu masu muhimmanci bane, kawai suna shigowa domin yiwa APCn Gombe zagon kasa.
"Amma a wannan batu na dan majalisa, muna tabbacin ingancin barinsa PDP tare da dawowa APC domin ba jam'iyyar gudunmawa a tafiyarta da zaben 2023."

Rikicin APC a Zamfara: Magoya Bayan Matawalle a Garinsu Sun Juya Masa Baya, Sun Koma Ɓangaren Marafa

A wani labarin, jiga-jigan jam’iyyar APC daga karamar hukumar Maradun, asalin garinsu Gwamna Bello Matawalle, sun bayyana goyon bayan su ga bangaren jam’iyyar na Sanata Kabiru Garba Marafa, The Punch ta ruwaito.

Jagororin su sun hada da Captain Halilu Haliru mai murabus da kuma tsohon darekta janar na ma’aikatan gwamnatin jihar, Malam Sale ST, wadanda suka yanke shawarar juya wa Matawalle baya akan gaza yi wa jihar aikin a zo a gani.

Bangaren da suka juya masa baya sun samu karbuwa zuwa bangaren APC na Sanata Marafa, inda Hon Bello Bakyasuwa ya amshe su hannu bibbiyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel