Rikici ya kai ga sojoji kashe jami'in tsaron farin kasa na DSS a cikin wani otal

Rikici ya kai ga sojoji kashe jami'in tsaron farin kasa na DSS a cikin wani otal

- Wasu sojoji sun hallaka wani jami'an tsaron farin kaya na DSS har lahira a wani otal a jihar Ekiti

- Rahotanni sun bayyana cewa, takaddama ce ta barka tsakaninsu, lamarin da ya jawo mutuwar jami'in

- Rundunar 'yan sanda ta jihar Ekiti ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma ce tana kan bincike har yanzu

Rahoto daga Daily Trust ya ce, wasu sojoji uku sun kashe wani jami'in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a wani otal da ke Ado-Ekiti.

Sojojin sun mamaye otal din ne da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Alhamis inda daya daga cikin sojojin ya dabawa jami’in DSS din wuka har lahira.

Karin bayanin da aka tattara ya nuna cewa lamarin ya faru ne sakamakon takaddama tsakanin sojoji da jami'in na DSS, bayan cafke wani matashi da ake zargi da aikata damfara ta yanar gizo a cikin otal din.

KU KARANTA: Ku kirkiri taku kafar: APC ta kalubalanci matasan Najeriya bayan hana Twitter

Sojoji sun kashe jami'in tsaron farin kasa na DSS a wani otal a jihar Ekiti
Sojoji sun kashe jami'in tsaron farin kasa na DSS a wani otal a jihar Ekiti Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jami'in na DSS yana kokarin shiga tsakani ne kan yunkurin da sojoji suka yi na kamo wanda ake zargin lamarin da ya jawo daya daga cikin sojojin ya fusata ya daba masa wuka har lahira.

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandar Jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Abutu ya bayyana cewa an kashe wanda aka kashen ne a yayin wata takaddama da wasu sojoji kuma ‘yan sanda suna bincike a kan lamarin.

Baya ga tabbatarwar hukumar 'yan sanda, wani ganau wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar The Nation cewa, jami’an DSS din an daba musu wuka a wuya kuma jini ya zuba sosai, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

KU KARANTA: Bayan shekaru 5 na aiki tukuru, beran da ya ci lambar yabon zinare ya yi ritaya

A wani labarin daban, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cafke wani yaro dan shekara 15 da ya dabawa matar dan uwansa 'yar shekara 25 wuka.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da DSP Abdullah Aaron, kakakin ‘yan sanda a jihar ya fitar., Daily Trust ta ruwaito.

DSP Haruna ya bayyana cewa: “Misalin karfe 11 na dare, an samu wani korafi cewa wanda ake zargin ya dabawa Misis Habiba Isah wacce ke dauke da ciki wata takwas wuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel