'Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Harbe Tsohuwar Jigon Jam'iyyar PDP Da Ƴaƴanta Mata 2

'Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Harbe Tsohuwar Jigon Jam'iyyar PDP Da Ƴaƴanta Mata 2

  • Wasu miyagun yan bindiga sun afka gidan tsohuwar shugaban mata na jam'iyyar PDP a Jihar Abia sun kai mata hari
  • Yayin harin, sun bindige ta har lahira sannan suke harbi yayanta mata biyu, daya ta mutu, daya kuma tana asibiti ana mata magani
  • Geoffrey Ogbonna mai magana da yawun yan sandan jihar Abia ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce suna jiran cikakken bayani a hukumance

Jihar Abia - Wasu miyagun yan bindiga sun kashe mutane hudu a karamar hukumar Ohafia ta Jihar Abia, rahoton Nigerian Tribune.

Mutane hudun da aka kashe sun hada da tsohuwar shugaban mata na PDP, Ucha Ndukwe, yar ta, Chibuzor Ndukwe da wasu biyu - Ndubisi Ndukwe da Kalu Umah.

Yan sanda a jihar sun tabbatar cewa an bindige su ne a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige tsohuwar shugabar matan PDP, diyarta da wasu mutum biyu

Yan Bindiga Sun Harbe Tsohuwa Shugaban Mata Na PDP da Yaranta a Gidansu
Yan Bindiga Sun Harbe Tsohuwa Shugaban Mata Na PDP da Yaranta a Gidansu. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban karamar hukumar Ohafia ya tabbatar da harin

Shima shugaban karamar hukumar Ohafia, Dr Okorafor Ukiwe, ya ce tafi cibiyar Lafiya ta tarayya da ke Umuahia, inda ya ke duba wani mara lafiyan da wata yar mamaciyar, Madam Ndukwe.

Ya ce matar da aka yi wa rauni ta rasa mahaifiyarta da yar uwarta da yan bindiga suka bindige su a gidansu.

"Yanzu aka gama mata tiyata aka ciro harsashin daga jikinta. Yan bindigan sun kashe mahaifyarta da yar uwarta a gidansu bayan kona shagon mahaifiyarta."

Ya cigaba da cewa wadanda ake zargin sun fusaa ne saboda matar, mai sayar da abinci bata goyon bayan abin da suke yi a unguwar, ya kara da cewa:

"Sun kona shagonta, suka zo gidanta sannan suka bindige ta kuma da yaranta biyu suka fito, suka harbe su.

Kara karanta wannan

Abuja: 'Yan bindiga sun hallaka 'yan mata biyu a hanyarsu ta zuwa biki

"Daya ta mutu nan take yayin da dayan kuma tana asibiti ana bata kulawa. Yan bindigan sun kuma kashe wasu maza biyu," in ji shugaban karamar hukumar.

Rundunar yan sanda sun yi martani game da lamarin

Kakakin yan sandan jihar Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa:

"Mun samu labarin abin amma muna jiran rahoto a hukumance da zai taimaka wa yan sanda sanin cikaken bayani."

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari, ta ce ba za a bada belinsa ba

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel