Zamfara: Ƴan Ta'adda Sun Kashe Mutum 8 Saboda Ƴan Uwansu Sun Gaza Biyan Kuɗin Fansa

Zamfara: Ƴan Ta'adda Sun Kashe Mutum 8 Saboda Ƴan Uwansu Sun Gaza Biyan Kuɗin Fansa

  • Wasu ‘yan bindiga da ke karkashin wani shu’umin shugaban su, Dankarami, sun halaka mutane 8 cikin mutane 10 da suka yi garkuwa da su
  • Hakan ya auku ne a Zurmi da ke Jihar Zamfara kuma lamarin ya biyo bayan gaza biyan kudin fansa, Naira miliyan 6 da suka nema a wurin ‘yan uwan wadanda suka sace
  • Sun sace su ne a ranar 1 ga watan Satumban 2021 bayan sun yi yunkurin kai hari hedkwatar karamar hukumar amma bai yiwu ba

Zamfara - ‘Yan bindigan da ke karkashin shugaban su, Dankarami sun halaka mutane 8 cikin 10 da suka sace tun watan Satumban shekarar 2021 yayin kai hari hedkwatar karamar hukumar amma bai yiwu ba, Premium Times ta ruwaito.

Sun halaka su ne sakamakon kasa biyan kudin fansar da suka bukata, N6m a wurin ‘yan uwan su kamar yadda mazauna yankin suka shaida.

Kara karanta wannan

‘Ƴan Daba’ Sun Sake Banka Wa Wata Ofishin Ƴan Sanda Wuta

Zamfara: Ƴan Ta'adda Sun Kashe Mutum 8 Saboda Ƴan Uwansu Sun Gaza Biyan Kuɗin Fansa
Zamfara: Ƴan Bindig Sun Kashe Mutum 8 Saboda Ƴan Uwansu Sun Gaza Biyan Kuɗin Fansa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan bindiga sun dade suna halaka jama’a kuma suna sace dubbannin jama’a a yankin arewa maso yamma da Jihar Neja tun shekarar 2021.

Mutum biyu sun tsira

Wani shugaban matasa na Zurmi, Abdullahi Muhammad ya sanar da wakilin Premium Times ta wayar salula cewa bayan makwanni biyu da sace su, 2 cikin 10 sun gudu daga maboyar ‘yan bindigan.

Kamar yadda ya ce:

“Ina cikin wadanda suka tarbi wadanda aka sace a ofishin karamar hukumar bayan sun gudo. Sun sanar da mu yadda suka dinga azabtar da su bayan ‘yan uwan su sun gaza biyan kudin fansa.”

Ya ce ‘yan bindigan sun samu lambobin wayar ‘yan uwan wadanda suka sace sannan suka fara tuntubar su.

Maharan sun halaka mutane takwas

Kamar yadda Muhammad ya shaida, ‘yan bindigan sun ci gaba da sauya yawan kudin fansar wadanda suka sace wanda hakan ne sanadin bata lokacin.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Kamar yadda ya ce:

“Mutane biyun da suka tsero da suka tsira. Sauran 8 din kuwa an azabtar da su har sai da suka mutu. Da farko sun ce N50m, suka koma suka bukaci N20m. Bayan nan basu sake kira ba sai bayan kwana 10.
Shugaban matasan yace sun ci gaba da barazana akan cewa matsawar ‘yan uwan basu kawo kudin ba zaisu jama’a cikin tashin hankali.”

Wadanda suka halaka

Premium Times ta bayyana sunayen wadanda suka halaka wadanda duk maza ne.

Akwai: Idi Mijin Hajia, Malam Zubairu, Murtala Nagoma, Umar Muhammad, Siddi Na Umara, Habibu DanBala, Yahaya Attaj da Zayyanu Nagoma.

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar, Mohammed Shehu, bai amsa kira da sakon da Premium Times ta tura masa ba.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Sarki a Jihar Arewa

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel