'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Sarki a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Sarki a Jihar Arewa

  • ‘Yan bindiga sun je har gidan wani basarake, Mai Martaba Dikyet Gupiya da ke Pushit a karamar hukumar Mangu a cikin Jihar Filato
  • Basaraken dagacin kauyen Pushit ne, garin su mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Sonni Tyoden, wanda dagacin kansa dan uwan mataimakin gwamnan ne na kusa
  • Wata majiya ta bayyana yadda lamarin ya auku jiya da dare da misalin karfe 9:05 lokacin dagacin yana tsaka da sauraron labarai inda suka yi awon gaba da shi

Filato - ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake da ke karamar hukumar Mangu a Jihar Filato, Mai martaba Dikyet Gupiya har cikin gidansa da ke Pushit, Vanguard ta ruwaito.

Basaraken dagacin kauyen Pushit ne, asalin garin su mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Sonni Tyoden, kuma dan uwan mataimakin gwamnan ne na kusa.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun shigo gidan Sarki cikin dare sun yi garkuwa da Mai martaba a Arewa

'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Sarki a Jihar Arewa
'Yan Bindiga Sun Sake Sace Sarki a Jihar Plateau. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta shaida yadda lamarin ya auku bisa ruwayar Vanguard:

“Sun yi garkuwa da shi jiya da dare da misalin karfe 9:05 yayin da yake tsaka da sauraron labarai. Sun wuce da shi inda babu wanda ya sani. Muna masa fatan tsira.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin

Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Gabriel Uba, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya shaida cewa:

“Eh, muna da masaniya dangane da satar basaraken mai daraja ta uku a Mangu. Yanzu haka mun tura jami’ai don su binciko inda yake kuma su ceto shi. Muna aiki tare da ‘Yan Sa kai tare da wasu don tabbatar da an ceto shi.”

Idan ba a manta ba an sace dagacin Gindiri da ke cikin karamar hukumar Mangu a jihar a watan Disamban da ya gabata, amma tuni masu garkuwa da mutanen suka sako shi.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Wadanda Suka Sace Dagaci Da Mutum 14 Sun Rage Kudin Fansa, Yanzu Sun Ce a Basu Buhun Shinkafa 2 Da N4m

A wani labarin, masu garkuwa da mutanen da suka sace dan dagacin kauyen Gwombe, Junaidu Danjuma da sauran mutane 14 a yankin Gwargwada da ke karamar hukumar Kuje a Abuja sun sauya bukatun su, Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu sun koma bukatar Naira miliyan 4 da buhunan shinkafa 2 maimakon Naira miliyan 15 da suka bukata da farko.

Daily Trust ta ruwaito yadda suka sace mutanen kauyen guda 11 ciki har da matar mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Gwargwada, Mrs Asabe Mohammed Koriya a ranar 4 ga watan Fabrairun 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel