Rashin tsaro: Dan takarar shugaban kasa ya je neman shawari wurin Sheikh Gumi

Rashin tsaro: Dan takarar shugaban kasa ya je neman shawari wurin Sheikh Gumi

  • Wani dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya gana da Sheikh Gumi a Kaduna kwanan nan
  • Momodu, mawallafin mujallar Ovation ya ce ya damu matuka da irin tabarbarewar yanayin tsaro a fitacciyar jihar ta Arewa
  • Momodu ya lura cewa malamin addinin Islaman ya yi nazari mai zurfi kuma mai kyau wanda za a iya amfani da shi wajen magance tsaro

Dele Momodu ya gana da Sheikh Ahmad Gumi, a jihar Kaduna dangane da matsalar rashin tsaro da ya yi kamari a jihar Kaduna wanda a da ya kasance birni mai wadata da aminci a Arewacin kasar.

A shafinsa na Instagram, dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa a kwanakin baya ya ziyarci Kaduna ne domin neman shawari daga malamin addinin Islaman kan hanyoyin magance matsalolin hare-hare da kashe-kashe a jihar.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Yadda jariri mai watanni 19 ya fada rijiya, ya nutse a jihar Kano

Dele Momodu ya gana da Gumi
Rashin tsaro: Dan takarar shugaban kasa ya je neman shawari wurin Sheikh Gumi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Momodu ya kara da cewa bincike da nazarin da Gumi ya yi kan al’amarin rashin tsaro ya kasance mai zurfi, da fa'idantarwa da za a iya fahimta.

Ya bayyana cewa, yunkurin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar shi ne kan gaba.

Ya koka kan yadda Kaduna ta sauya, inda yace a da gari ne mai yawan Janar-Janar na sojojin kasar.

Kana ya koka kan yadda Kaduna ta sauya ta zama daya daga cikin jihohin da a Arewa ake fama da matsalolin tsaro.

A bangare guda, ya yaba wa Sheikh Gumi, inda yace yana daga cikin wadanda ke sharhi kan abubuwan da suka shafi lamurran tsaro a kasar nan.

Bangaren Sheikh Gumi ya maida martani kan kashe shugabannin yan bindiga a Zamfara

Kara karanta wannan

Duk za mu mutu: Yaro ya fashe da kuka, yana tsoron ka da Rasha ta harbo bam Najeriya

A wani labarin daban, yayin da yan Najeriya ke murnan nasarar da sojiji suka samu a Zamfara na kashe shugabannin yan binidga, sansanin shahararren malamin nan, Sheikh Gumi, ya nuna tantama kan lamarin.

Bangaren Malamin, waDanda ke ganin hanyar sulhu ce kaɗai mafita, ya yi kira ga rundunar soji ta tabbatar da ikirarinta ta hanyar bayyana hujjoji.

Jaridar Vangaurd ta rahoto Daya daga cikin mambobin bangaren Gumi, Dan Iyan Fika a jihar Yobe, Alhaji Tukur Mamu, na cewa ya kamata mutane su tambayi kansu ina shaidar kashe yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel