Tsautsayi: Yadda jariri mai watanni 19 ya fada rijiya, ya nutse a jihar Kano

Tsautsayi: Yadda jariri mai watanni 19 ya fada rijiya, ya nutse a jihar Kano

  • Wani mummunan yanayi ya faru a jihar Kano, wani jariri ya fada rijiya ya nutse, lamarin da ya kai ga mutuwarsa
  • An yi nasarar cire yaron daga cikin rijiyar, amma an samu ya riga da ya mutu, lamarin da ya jawo alhini ga iyayen
  • Rundunar hukumar kashe gobara ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ta ce ita ta ciro yaron daga rijiyar budaddiya

Danbatta, jihar Kano - Jaridar Daily Trust ta ruwaito faruwar wani mummunan lamari a jihar Kano ranar Talata yayin da wani jariri dan watanni 19 ya nutse a cikin rijiya da ke unguwar Al-Ansar da ke karamar hukumar Danbatta a jihar.

Lamarin da ya yi sanadin mutuwar jaririn ya faru ne a lokacin da mahaifiyarsa ta yi dan nisa da bakin rijiyar.

Mutuwar yaro a jihar Kano cikin rijiya
Hawaye na kwaranya yayin da yaro dan wata 19 ya fada rijiya, ya mutu a Kano | Hoto: thenationonlineng.com
Asali: UGC

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya ce sun samu kiran gaggawa daga wani Salisu Bello inda suka aika da tawagar agaji zuwa wurin.

Kara karanta wannan

Duk za mu mutu: Yaro ya fashe da kuka, yana tsoron ka da Rasha ta harbo bam Najeriya

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Rundunar ta fitar da gawar yaron matacce daga cikin rijiyar hakazalika hukumar ta fara binciken lamarin."

Abdullahi ya kara da cewa an mika gawar yaron ga kakansa, Malam Abdulkadir domin binne shi.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su kula da ‘ya’yansu domin gujewa irin wannan mummunan yanayi mara dadi, ya kara da cewa bai kamata a rika barin yara su kadai ba ko ta halin kaka.

Hakazalika, ya umurci mazauna yankin da su yi kokarin gina katangu masu tsayi a bakin budaddun rijiyoyinsu da kuma samar da marufi domin rufe su a ko da yaushe, kamar yadda PM News ta tattaro.

Yajin aikin Likitoci: Sabon jariri ya mutu a asibiti sakamakon rashin Likita

A wani labarin, mutuwar wani sabon jariri a asibitin koyarwan jami'ar Legas (LUTH) sakamakon yajin aikin da Likitocin Najeriya ke yi ya janyo cece-kuce a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Wani mutumi mai suna Vincent Abuladan ya bayyana yadda surukarsa ta samu mishkila yayin nakuda kuma aka rika yawo da ita daga asibiti zuwa asibiti amma babu Likitoci har inda yaron ya mutu a asibitin LUTH.

A cewar TheCable, Vincent ya daura laifin mutuwar sabon jaririn kan rashin Likitoci a asibitocin da suka je.

Asali: Legit.ng

Online view pixel