Bidiyon matan gwamnoni a ziyarar Aisha Buhari da suka yi Dubai,sun bata kek na bazday

Bidiyon matan gwamnoni a ziyarar Aisha Buhari da suka yi Dubai,sun bata kek na bazday

  • Matan gwamnoni sun kai wa Aisha Buhari ziyara a Dubai tare da kek suna taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta a wani bidiyo
  • Matan sun rera mata waka, yayin da hasken kamara ya haska ko ina a kasaitaccen dakin da aka sauki bakin daga Najeriya
  • 'Yan Najeriya da dama sun yi mamakin cewa gwamnatin ce ta dauki nauyin tafiyar mayalwatan matan gwamnonin ba

A wani bidiyo da yayi yawo a kafafen sada zumunta, an nuna ziyarar da matan gwamnoni suka kai wa Aisha Buhari a Dubai tare da kek.

Suna taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta, wanda ya jawo cece-kuce daga 'yan Najeriya da dama a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, a lokacin da ake tsaka da karancin man fetur da yajin aikin ASUU.

Bidiyon matan gwamnoni a ziyarar Aisha Buhari da suka yi Dubai,sun bata kek na bazday
Bidiyon matan gwamnoni a ziyarar Aisha Buhari da suka yi Dubai,sun bata kek na bazday. Hoto daga @henryshield
Asali: Twitter

Legit.ng ta lura da cewa, bikin zagayowar ranar haihuwar matar shugaban kasar na asali a watan Janairu ne, kuma a sirrance take shagalin.

Kara karanta wannan

Sabon jidali: Tallafin mai zai karu kan FG yayin da farashin mai ya tashi zuwa $112.7 kan kowacce ganga

Dukkan matan gwamnonin sun rerawa Aisha Buhari waka. Matan sun jeru a kayataccen dakin, inda suke tohowa zuwa ga Aisha a jere, suna rera mata wakar murnar zagayowar ranar haihuwar ta.

Fuskar su na bayyana farin ciki a hotuna, yayin da kamara ke haska kowanne lungu da sako na dakin, a lokacin da fuskar matar shugaban kasar ke dauke da murmushi da annashuwa, sannan ta rungume wasu daga cikin su.

Wannan bidiyon ya tattara daruruwan tsokaci, bayan @henryshield ya sake wallafa shi a Twitter.

Tsokacin 'yan Najeriya

Ga wasu daga cikin tsokacin:

@MummyKachi ta ce: "Tsananin rashin daraja, Uwar wasu."
@RealMrKay ya ce: "Ba ni da matsala idan Aisha Buhari ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta. Damuwa ta shi ne yadda suka mayar da Dubai babban birnin Najeriya. A Najeriya ne kadai matar shugaban kasa za ta yi fatali da kasar ta zuwa wata wawuyar kasa."

Kara karanta wannan

Budurwa ta gwangwaje matashi dake doguwar tafiya zuwa makatanta da dalleliyar mota

@Niellsbaba ya ce: "A wurin su babu yajin aiki, tunda bai shafi yaran su ba."
@MayorDeWriter ya ce: "Kawai saboda kek! Kusan su 12 suka kwashi jiki suka tafi Dubai! cabdi jam."
@Yusuf__jr ya ce: "Bayan kallon wannan bidiyon, za ka yi zaton wadanda suke mulka suna cikin farinciki."
@PapaEngagement ya ce: "Maganar gaskiya ba ni da matsala da wannan, tsaka-tsakin 'yan Najeriya da dama suna zuwa Dubai, US da sauran kasashe don wannan dalilin. A bayyane yake tana da kudin da za ta da kuma kudin Najeriya. Amma me zai sa matan gwamnoni tafiya har dubai don su bata kek?"

Hotunan 'ya'yan Buhari a wani taro tare da 'dan takarar shugabancin kasa

A wani labari na daban, gagarumin taron karramawa da bayar da lambar yabo da kungiyar 'yan jarida mata ta Najeriya ta shirya a ranar Alhamis da ta gabata ya samu halartar manyan mutane a sassa daban-daban na fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

An shirya wannan taron ne domin karrama nasarorin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, wacce ta samu wakilcin 'ya'yanta mata, Halima Buhari-Sheriff da Zahra Buhari-Indimi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel