Ramadan: Dakatar da jirgin kai tsaye zuwa Saudiyya na iya hana 'yan Najeriya Umrah a Azumi, CSO

Ramadan: Dakatar da jirgin kai tsaye zuwa Saudiyya na iya hana 'yan Najeriya Umrah a Azumi, CSO

  • Ana fargabar 'yan Najeriya za su rasa damar yin aikin Umrah a watan Ramadana saboda wata dokar hana shiga kasar
  • Wannan fargaba na zuwa ne daga wata kungiyar farar hula mai alaka da jigilar ayyukan hajji da Umrah a Najeriya
  • Kungiyar ta bayyana irin abubuwan da take fargaba, inda tace ya kamata a duba yiwuwar warware wannan baraka

Daily Trust ta rahoto cewa, wata kungiyar farar hula ta koka game da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye zuwa Saudi Arabiya saboda Korona, gashi kuma saura kwanaki 30 a shiga watan Ramadan.

A cikin wata sanarwa da kodinetan kungiyar, Ibrahim Muhammed a Kaduna ya fitar ta bayyana cewa ci gaba da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya kai tsaye da gwamnatin Saudiyya ta yi na iya kawo cikas ga maniyyata Umrah daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Mun shirya: Najeriya za ta fara gina tashar makamashin nukiliya, ta hada kai da Rasha, da wasu kasashe

Aikin Umrah zai zama wahala ga 'yan Najeriya
Ramadan: Dakatar da Jirgin kai tsaye zuwa Saudiyya na iya hana 'yan Najeriya Umrah | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A can baya kungiyar ta ce, masu gudanar da aikin jigilar Hajji a Najeriya sun yi asarar biliyoyi a dalilin haramcin, kamar yadda Blueprint ta rahoto.

Idan dai za ku tuna, Masarautar Saudiyya ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jirage a cikin wata takardar da ta aikewa dukkanin kamfanonin jiragen sama da ke aiki a kasar a watan Disamban bara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga baya gwamnatin tarayya ta roki kasar Saudiyya da ta dage takunkumin hana zirga-zirgar da ta sanya wa matafiya ‘yan Najeriya biyo bayan bullar Koronan omicron a Afirka ta Kudu da aka gano a tsakanin wasu matafiya da aka ce sun ziyarci Najeriya.

Tabbas akwai aikin Hajji a shekarar 2022, Maniyyata su shirya, NAHCON

A wani labarin, kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga da kuma yaɗa labarai na hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Sheikh Prince Suleman Mamoh, yace bana yan Najeriya zasu samu damar sauke farali a kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

Bidiyon matan gwamnoni a ziyarar Aisha Buhari da suka yi Dubai, sun bata kek na bazday

Prince Mamoh ya bayyyana cewa babu tantama suna da tabbacin wannan shekarar 2022, maniyyata zasu gudanar da Hajji.

Da yake fira da Legit.ng Hausa, kwamishinan ya yi kira ga maniyyata dake faɗin Najeriya su fara shiri tun yanzun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel