Da Duminsa: Shugaba Buhari ya amince da fitar da makudan kudade na kwaso yan Najeriya daga Ukraine

Da Duminsa: Shugaba Buhari ya amince da fitar da makudan kudade na kwaso yan Najeriya daga Ukraine

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ware makudan kudade domin aikin dawo da yan Najeriya gida daga Ukraine
  • Karamin minista a ma'aikatar harkokin waje, Zubairu Dada, ne ya faɗi haka jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa a Abuja
  • Ya ce jirage uku da zasu yi aikin zasu bar Najeriya zuwa kasashe huɗu dake makwaftaka da Ukraine

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da ware dala miliyan $8.5m ga ma'aikatar harkokin waje da ma'aikatar jin kai da walwalar al'umma domin jigilar yan Najeriya da suka makale a Ukraine.

Channels tv ta rahoto cewa Gwamnatin Buhari ta kammala shirin kwaso yan Najeriya 5,000 waɗan da rikicin Rasha da Ukraine ya rutsa da su.

Ƙaramin ministan harkokin ƙasashen waje, Zubairu Dada, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya dira birnin Nairobi, inda daga nan zai tafi Landan ganin Likita

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Da Duminsa: Shugaba Buhari ya amince da fitar makudan kudade na kwaso yan Najeriya daga Ukraine Hoto: Freedom Radio Nigeria/Facebook
Asali: Facebook

Ministan ya shaida wa masu ɗakko rahoton gidan gwamnati jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa cewa za'a tashi jiragen sama uku zuwa ƙasashe hudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ƙasashen da jiragen da zasu yi aikin kwaso yan ƙasa zasu nufa sune Poland, Hungary, Slovakia, da Romania, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Jirage biyu daga kamfanin Air Peace da kuma guda ɗaya da kamfanin Max Air ne ake tsammanin zasu gudanar da aikin jigilar dawo da mutanen gida.

Mista Dada ya yi bayanin cewa tuni aka ware wa hukumomi kuɗaɗe domin tabbatar da an fara wannan muhimmin aiki ranar Laraba.

Ya ce:

"Gwamnati ta fitarwa hukumomin dake da alhakin aikin kudade domin tabbatar da fara jigilar dawo da mutane gida ranar Laraba."

Kazalika gwamnatin tarayya ta sanar da cewa Jiragen zasu yi aikin jigilar ne bisa yadda aka tsara musu har zuwa lokacin da za'a kammala baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe yan kasarta da yaki ya ritsa da su a Ukraine

A wani labarin na daban kuma hankulan yan kallon kwallo ya tashi yayin da aga gano Bam a wurin da suke kallo a Kaduna

Bayan samun rahoto, kwararrun jami'an yan sanda na sashin kwance abin fashewa suka dira wurin, kuma suka yi nasarar cire shi.

A baya, gwamnatin Kaduna ta gargaɗi mazauna jihar su sanya ido kan abubuwan dake wakana a zagayen su, kuma su kai rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel