Da duminsa: Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe yan kasarta da yaki ya ritsa da su a Ukraine

Da duminsa: Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe yan kasarta da yaki ya ritsa da su a Ukraine

Ofishin Jakadancin Najeriya dake Warsaw, birnin kasar Poland ta fara kwashe yan Najeriya da yaki ta ritsa dasu a kasar Ukraine daga iyakan kasar da Poland.

TheCable ta ruwaito cewa Jakadan Najeriya dake kasar Poland, C. O Ugwu, ke jagorantar kwasan.

An ce an fara hakan ne tun ranar 26 ga Febrairu.

Yakin Rasha da Ukraine ya tilastawa yan Najeriya guduwa daga kasar zuwa kasashen dake makwabtaka da ita.

Sakamakon haka yan Najeriya suka fara guduwa kasar Poland, Hungary, da Romania.

Kalli hotunansu:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ukraine
Da duminsa: Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe yan kasarta da yaki ya ritsa da su a Ukraine Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Ukraine
Da duminsa: Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe yan kasarta da yaki ya ritsa da su a Ukraine Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Da duminsa: Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe yan kasarta da yaki ya ritsa da su a Ukraine
Da duminsa: Gwamnatin Najeriya ta fara kwashe yan kasarta da yaki ya ritsa da su a Ukraine Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Gwamnatin Buhari zata fara jigilar dawo da yan Najeriya gida daga Ukraine

Gwamnatin tarayya zata fara jigilar dawo da yan Najeriya da suka maƙale a rikicin Rasha da Ukraine gida.

Kara karanta wannan

Wasu yan Najeriyan da muke kokarin kwasowa daga Ukraine sun ce ba zasu dawo ba, Minista waje

Ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, shi ne ya bayyana haka yayin ganawa da kakakin majalisar dokokin tarayya, Femi Gbajabiamila, ranar Litinin.

A wani sako da kakakin ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce gwamnati zata fara aikin dawo da yan ƙasarta gida Najeriya ranar Laraba.

Ministan ya ce Najeriya ta kammala duk wasu shirye-shiryen dawo da yan ƙasa gida, waɗan da suka keta zuwa wasu ƙasashen saboda yaƙin Rasha-Ukraine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel