An kore shi daga aiki bayan matarsa ta zagi shugabansa, ta kwashe kudadensa ta tsere

An kore shi daga aiki bayan matarsa ta zagi shugabansa, ta kwashe kudadensa ta tsere

  • Wani matashi mai suna Oscar Constant Ouma, ya je kafar sada zumunta inda yake neman taimako bayan ya rasa aikin da yake a banki
  • Ya taba aure a baya kuma yana aiki a banki amma kwatsam wata rana aka kore shi bayan matarsa ta zage shugabar shi a wurin aiki
  • Mutumin mai fama da cutar asma ya sake shiga tashin hankali bayan ya koma gida ya tarar matarsa ta kwashe komai nata da kudin da yake tarawa ta gudu

Wani matashi mai shekaru 31 mai suna Oscar Constant Ouma ya bayyana rokonsa a kafar sada zumunta ta Kenya kan a taimaka masa da aiki inda ya kara da cewa a kan kwalayensa na karatu kullum yake bacci

Ouma ya kammala digirinsa ne daga jami'ar Egerton ta Kenya a 2013 amma kwata-kwata yanzu yana cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani mutum ya daba wa mahaifiyarsa wuka har lahira yayin da yake fada da matarsa a Neja

An kore shi daga aiki bayan matarsa ta zagi shugabansa, ta kwashe kudadensa ta tsere
An kore shi daga aiki bayan matarsa ta zagi shugabansa, ta kwashe kudadensa ta tsere. Hoto daga @ConstantOscar
Asali: Twitter

Matarsa ta zagi manajarsa

A wata tattaunawa da Tuko tayi da matashin dan asalin Kisumu, ya bayyana cewa ya taba aiki da bankin KCB a baya kuma ya rasa aikinsa ne sakamakon zagi irin na matarsa.

Kamar yadda yace, matarsa ta zagi manajarsa mace wanda hakan yasa aka kore shi daga aiki.

"Na bar wayata a kan tebur kuma na shiga bandaki yayin da manajata ta turo min sakon kar ta kwana inda ta ke tambaya ko zan iya aiki ranar Asabar. Tunda ban taba zuwa aiki a ranakun karshen mako ba, matata ba ta yarda ba don haka ta dauka lambarta ta kira ta," yace.

Ouma ya ce lokacin da matarsa ta ji muryar mace, ta dinga auna mata zagi kafin ta tsunbula wayarsa a ruwa.

Kara karanta wannan

Dankareriyar amarya ta nuna bajinta wurin rawa tare da dan tsurut din angonta a wani bidiyo

An mika masa takardar kora daga aiki

Litinin ta gaba, Ouma ya je aiki ba tare da ya amsa kiran manajarsa ba, har da zagin da matar ta yi mata a waya.

"Kawai na gane hakan ne bayan an mika min takardar kora daga aiki," yace.

Ko bayan ya rasa aikinsa, ya yafe wa matarsa kuma ya koma Nakuru tare da ita inda yake aikin leburanci.

Tun farko yana da cutar asma don haka ne baya iya daukar kayan nauyi ko kuma shakar kura mai yawa.

"Ko bayan a bani aiki, dole na bar shi saboda suna tsoron zan iya rasa rayuwata. Bayan an biya ni kudin aikin kuma, a magani yake karewa," ya kara da cewa.

Baccinsa yake sha a kan takardun karatunsa

A wani yammaci, Ouma ya dawo daga fafutuka ya samu babu kowa a gidansa. Matarsa ta kwashe komai ta tsere har da kudin da yake tarawa.

Kara karanta wannan

Jaruma Hafsat Idris ta magantu a kan batun aurenta, hoton matashin mijinta ya bayyana

Wannan al'amarin ne yasa ya fada damuwa har ya kai ga an mika shi gidan mahaukata na wata shida saboda ya samu daidaituwa.

Lokacin da ya koma gida, ya kasa gane inda ya dosa a rayuwarsa inda yake ta kokarin manta baya.

A halin yanzu yana kwanciya ne a kan takardun karatunsa tare da fatan wata rana komai zai warware.

Kotu ta tsinke aure bayan mata ta kama mijinta turmi da tabarya da wata, kuma ya zaneta saboda ta koka

A wani labari na daban, a ranar Alhamis wata kotu a Igando ta biya wa wata matar aure, Isoboye Dominics bukatar raba auren ta da mijin ta, Christopher saboda ta kama shi suna lalata da wata.

A hukuncin da Alkali Koledoye Adeniyi, ya yi amfani da rashin halartar kotun da Christopher yayi don kare kansa, Premium Times ta ruwaito.

"Akwai ban takaici matuka irin yadda mai korafin ta fuskanci cin mutunci da matsananciyar damuwa daga hannun wanda ake karar. Auren ya samu tangarda ne, saboda wanda ake karar baya abun da ya kamata sai zama makwadaici da yayi."

Kara karanta wannan

Kotu ta tsinke aure bayan mata ta kama mijinta turmi da tabarya da wata kuma ya zaneta saboda ta koka

Asali: Legit.ng

Online view pixel