Kotu ta tsinke aure bayan mata ta kama mijinta turmi da tabarya da wata, kuma ya zaneta saboda ta koka

Kotu ta tsinke aure bayan mata ta kama mijinta turmi da tabarya da wata, kuma ya zaneta saboda ta koka

  • Wata kotun gargajiya da ke zama a Ikotun a jihar Legas ta tsinke aure sakamakon kama mijin da matar tayi turmi da tabarya da wata, kuma ya zaneta saboda yin korafi
  • Kamar yadda matar ta sanar, mijinta mai mugun kwadayi ne domin da mahaifiyarta ya dogara kuma take ciyar da su
  • Alkalin kotun ya yi amfani da rashin halartar kotun da mijin yayi inda ya karba bukatar matar na cewa a bata rainon yaran da suka haifa bayan tsinke auren

A ranar Alhamis wata kotu a Igando ta biya wa wata matar aure, Isoboye Dominics bukatar raba auren ta da mijin ta, Christopher saboda ta kama shi suna lalata da wata.

A hukuncin da Alkali Koledoye Adeniyi, ya yi amfani da rashin halartar kotun da Christopher yayi don kare kansa, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rayuwar aure: Yadda wata kotu ta gimtse auren da yayi shekaru 7 saboda sabani tsakanin ma'aurata

Kotu ta tsinke aure bayan mata ta kama mijinta turmi da tabarya da wata, kuma ya zaneta saboda ta koka
Kotu ta tsinke aure bayan mata ta kama mijinta turmi da tabarya da wata, kuma ya zaneta saboda ta koka. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: Facebook

"Akwai ban takaici matuka irin yadda mai korafin ta fuskanci cin mutunci da matsananciyar damuwa daga hannun wanda ake karar. Auren ya samu tangarda ne, saboda wanda ake karar baya abun da ya kamata sai zama makwadaici da yayi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan aka duba shaidun mai karar, za a gane cewa, wanda ake karar bai shirya daukar dawainiyar iyali a matsayinsa na miji sannan mahaifi ba, sai barin ragamar da yayi ga mahaifiyar matarsa, wacce ke da hannu da shuni.
"Baya ga haka, akwai shakku akan tabbacin kaunar da yake wa matarsa. Hakan yasa auren ya zama na jari, domin wanda ake karar kwadayin dukiyar sirikar tasa kawai yake.
"Idan har an za a iya samun wanda ake karar da laifin lalata bayan yana da mata, hakan alamace dake nuna baya kaunar matarsa, wanda hakan shaida ne na cin zarafin matarsa da yake," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame magidanci a gidan yari bayan ya kara aure babu sanin uwargidansa

Premium Times ya ruwaito cewa, Mai shari'ar ya kara da cewa, tilas ne a damka wa mai karar yaran guda biyu.

Ya kara da umartar Christopher da ya dinga bawa mai karar N20,000 duk wata don kula da kanta, sannan a bata damar ganawa da yaran a yardajjen wurin da dukan su suka amince.

Haka zalika, ya umarci wanda ake karar da ya biya N200,000 a matsayin kudin rabuwa, wanda zai biya ta hannun kotun.

"Za a dauki karya daya daga cikin dokokin da kotu ta gindaya a wasa da hankalin shari'a, wanda zai yi sanadiyyar yanke hukuncin wata shida a gidan yari ba tare da tara ba," ya tabbatar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito yadda mai karar, wacce take zaune a Ikotun ta bayyana gaban kotu a ranar 14 ga watan Oktoban 2021, tana mai rokon kotu da ta raba auren ta da mijinta, sannan ta bata damar kulawa da yaran ta.

Kara karanta wannan

Bai hallata mace 'yar sanda ta dau juna biyu ba muddin ba tada aure, Kotu ta yanke

Ta bayyana yadda ta kama mijinta dumu-dumu da wata mata suna lalata a dakin Otal, yayin da ta fuskance shi da maganar, ya nada mata bakin duka.

Hakan yasa ta roki kotu da ta raba auren, saboda yadda ta cigaba da shan duka, cin zarafi da rashin samun soyyaya da kulawa daga mijinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel