Jaruma Hafsat Idris ta magantu a kan batun aurenta, hoton matashin mijinta ya bayyana

Jaruma Hafsat Idris ta magantu a kan batun aurenta, hoton matashin mijinta ya bayyana

  • An daura auren jaruma Hafsat Idris wacce aka fi sani da Barauniya a garin Kura dake Kano a ranar Asabar da ta gabata
  • Ba kamar wasu daga cikin abokan sana'arta ba, Hafsat ta yi wuff da wani kyakyawan matashi ne mai suna Mukhtar
  • Bayan amarcewar jaruma Hafsat Idris, ta fito ta musanta alakar sabon mijinta da gidan Janar Abacha da ake ta yadawa

Alamu na nunawa watan Fabrairu da na Maris watannin baje-kolin bukukuwa ne a Kannywood, wanda bayan auren-auren da muka tattaro muku rahoto, sai kwatsam ga na jaruma Hafsat Idris wanda aka yi shi a cikin sirri.

Amma kuma duk yadda aka kai ga boye al'amarin sai da labarin ya bayyana.

Jaruma Hafsat Idris ta magantu a kan batun aurenta, hoton matashin mijinta ya bayyana
Jaruma Hafsat Idris ta magantu a kan batun aurenta, hoton matashin mijinta ya bayyana. Hoto daga @diaryofnorthernwoman
Asali: Instagram

A labarin da Legit.ng ta samu, an daura auren ne ba tare da daukar wani dogon lokaci ba kuma ba tare da yin wasu bukukuwa ba wanda ta yuwu sai za a tare sannan a sha shagalin.

Kara karanta wannan

Jaruma Ta Magantu Bayan Alƙali Ya Umarci a Sake Kama Ta

Jarumai kamar su Falalu A. Dorayi, Ali Nuhu, Maryam Booth da sauransu sun taya ta murna ta hanyar wallafa hoton ta a shafukansu gami da yi mata addu'a da fatan alkhairi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Labari ya bayyana cewa jarumar ta auri wani matashi ne ba babban mutum ko dattijo ba kamar yadda da yawan 'yan fim ke yi.

Ta aura matashi mai suna Mukhtar wanda aka daura auren a ranar Asabar a garin Kura da ke jihar Kano.

Yayin da jama'a ke taya ta murna ana kuma yada batun auren, wasu sun bayyana cewa angon nata yana da alaka da tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Sani Abaacha, lamarin da amaryar ta fito ta musanta a shafinta na Instagram.

"Assalamu alaikum, ina mika sakon godiyata ga dukkannin masoya, 'yan uwa da abokan arziki na fatan alkhairi da suka yi min.

Kara karanta wannan

Bazawara ta maka mahaifinta a kotu, ta ce karo na 3 kenan da yake mata auren dole

"Sai dai ina son na yi magana akan rade-radin da ke yawo musamman bloggers da ke rubutu a kai da cewa mijin da na aura yana da alaka da gidan Abacha, toh wannan ba gaskiya bane. Ba shi da alaka da su. Nagode," ta wallafa.

Tamfatsetsiyar sarkar miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikar ta

A wani labari na daaban, a kwanaki kadan da suka gabata ne aka yi sunan jikar Hafsat Idris inda jaririyar ta ci sunan Hafsat Junior.

Sai dai shagalin sunan ya dauka hankali matuka duba da yadda wani bikin auren bai kai shi tara jama'a da tsaruwa ba, musamman jaruman Kannywood mata da suka cika wurin kuma aka yi bushasha.

Mahaifiyar mai jegon ta yi fitar kece raini inda ta saka wani tsadajjen leshi dan ubansu da sarkar gwal da aka yi kiyasin kudin ta ya kai naira miliyan 11.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya za ta shiga daga ciki a ranar Juma'a mai zuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel