Tashin hankali: Wani mutum ya daba wa mahaifiyarsa wuka har lahira yayin da yake fada da matarsa a Neja

Tashin hankali: Wani mutum ya daba wa mahaifiyarsa wuka har lahira yayin da yake fada da matarsa a Neja

  • Wata uwa ta rasa ranta a yayin da take kokarin shiga tsakani bayan rikici ya kaure tsakanin danta da matarsa
  • Dan nata ne ya soke ta bisa kuskure a yayin da yake kokarin burma wa matar tasa wukar
  • Tuni dai aka damke magidancin wanda a yanzu matar tasa ke kwance a asibiti sakamakon mugun dukan da ya yi mata

Niger - Wani magidanci ya shiga hannu bayan ya daba wa mahaifiyarsa wuka bisa kuskure a Zawiyya Tudunwada da ke garin Kontagora, jihar Neja.

An tattaro cewa magidancin na fada ne da matarsa lokacin da mahaifiyar tasa ta iso domin shiga tsakani.

Tashin hankali: Wani mutum ya daba wa mahaifiyarsa wuka har lahira yayin da yake fada da matarsa a Neja
Tashin hankali: Wani mutum ya daba wa mahaifiyarsa wuka har lahira yayin da yake fada da matarsa a Neja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ana haka ne, sai mutumin ya dauko wuka sannan ya yi yunkurin daba wa matarsa, amma sai aka yi rashin dace ya soki mahaifiyarsa wacce ke kokarin raba fadar tasu, shafin Linda Ikeji ya rawaito.

Kara karanta wannan

Budurwa ta gwangwaje matashi dake doguwar tafiya zuwa makatanta da dalleliyar mota

Duk da kokarin da aka yi don ganin an ceto ta, mahaifiyar tasa ta mutu jim kadan bayan ya soke ta.

Hakazalika an kwashi matar wacce ta ji raunuka daban-daban sakamakon dukan da mijin ya yi mata zuwa asibiti.

Rahoton ya kuma kawo cewa an kama magidancin bayan labarin mutuwar mahaifiyar tasa ya fita.

Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya

A wani labarin, mun ji cewa wata matar Aure mai suna, Atika, ta daba wa maigidanta wuka har lahira a Mararaba, karamar hukumar Karu, jihar Nasarawa.

Lamarin kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya auku ne ranar Asabar da daddare yayin da magidancin ya shiga ɗakin matar.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Magidancin mai suna Ibrahim Salihu, ɗan kimanin shekara 37, ya shiga ɗakin Atika, wacce ita ce matarsa ta farko, domin mata bankwana ya koma ɗakin ɗayar matarsa da suke rayuwa a gida ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel