Dankareriyar amarya ta nuna bajinta wurin rawa tare da dan tsurut din angonta a wani bidiyo

Dankareriyar amarya ta nuna bajinta wurin rawa tare da dan tsurut din angonta a wani bidiyo

  • Kyakyawar amarya ta nuna bajintar ta yayin da ta girgije ta kwashi rawa a aurenta duk da kibarta da ta gawurta
  • Budurwar mai kiba ta bada mamaki inda ta riko angonta 'dan tsurut wanda ko kusa ba za a hada kibarsu ba
  • Ta dinga rawa a doguwar rigarta inda hannunta ya dinga bi tare da nuni da yadda wakar ta ke tafiya

A wani bidiyo da ya bayyana, an ga wata amarya dankareriya da ke kwasar rawa a tsakiyar filin aurensu duk da girman jikinta.

Angon da ya saka kayan gargajiya, ya taya amaryarsa burge mutane da irin rawarsa yayin da suke rausayawa ga wata wakar Pana wacce mawaki Tekno ya rera.

Dankareriyar amarya ta nuna bajinta wurin rawa tare da dan tsurut din angonta a wani bidiyo
Dankareriyar amarya ta nuna bajinta wurin rawa tare da dan tsurut din angonta a wani bidiyo. Hoto daga @bellanaijaweddings
Asali: Instagram

Angon dan tsurut a bayyane yake ya fi amarya iya rawa amma jikinta ne ya kara wa rawan armashi a wurin.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

A bidiyon mai kayatawar da @bellanaijaweddings suka wallafa a shafinsu na Instagram, budurwar da ke sanye da doguwar riga da ke jan kasa ta dinga nuni da hannayenta domin su bada irin yanayin wakar da ke tashi.

A wani lokaci kuwa, angon ya zo kusa da amarya inda yake dubanta cike da shauki da soyayya.

Mahaifiyata da mijina sun yi shekaru 15 suna lalata: Mata ta fashe da kuka yayin bada labari a bidiyo

A wani labari na daban, a lokacin da Soipan Martha take girma, ta yi burin samun soyyayar mahaifiyar ta, sai dai bata taba fahimtar dalilin da yasa hakan bai samu ba.

Lokacin tana 'yar shekara biyu, mahaifiyarta ta barta karkashin kulawar yayar ta, sannan ta tafi Saudi Arebiya don neman arzikin duniya. Ta bayyana yadda rayuwa bata mata dadi ba, yayin da take tunanin lokacin da za ta kara ganin mahaifiyar ta.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Wata rana, mahaifiyarta ta dawo daga Kenya, inda ta yanke shawarar kai ta makarantar kwana, amma babu mai kai mata ziyara a ranar da ake kai ziyara. Hakan yasa ta samu kusanci da shugabar makarantar, wacce ta sha alwashin rike ta kamar ita ta haife ta kuma tayi hakan.

Da taimakon kakarta, ta shiga makarantar sakandari bayan kammala firamaren, da haka ne ta fara aiki a sashin karamci, inda ta hadu da wani mutum, har suka fara soyayya. A rashin sa'a, ta fada soyyaya da mutumin banza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel