Buhari Ya Hassala, Ya Lashi Takobin Kare Ɗalibai Daga Masu Garkuwa Da Mutane

Buhari Ya Hassala, Ya Lashi Takobin Kare Ɗalibai Daga Masu Garkuwa Da Mutane

  • Shugaba kasa, Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati ta dauki tsauraran matakai akan masu garkuwa da mutane
  • Kamar yadda ya shaida, gwamnatin ta jajirce don kawo karshen garkuwa da yara musamman masu zuwa makaranta hakan yasa ya bukaci jama’a su taka tasu rawar
  • Ya yi wannan bayanin ne yayin jawabi a wani taro na jami’an tsaro wanda kungiyar tsofaffin daliban kwalejin tsaro, AANDEC ta kasa ta shirya a Abuja ranar Talata

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa an dauki saabin matakai masu tsauri kan matsalar garkuwa da mutane musamman wacce ta shafi yara masu zuwa makaranta, The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, gwamnati ta zage damtse wurin ganin karshen wannan matsalar. Buhari ya bayar da wannan tabbacin ne a wani taron jami’an tsaro wanda tsofaffin daliban kwalejin tsaro (AANDEC) ta shirya a ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Buhari Ya Hassala, Ya Lashi Takobin Kare Ɗalibai Daga Masu Garkuwa Da Mutane
Buhari Ya Lashi Takobin Kare Ɗalibai Daga Masu Garkuwa Da Mutane. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

An samu wannan bayanan ne a wata takarda wacce kakakinsa, Femi Adesina ta saki mai taken, ‘Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya su shiga cikin harkokin tsaro, ya yaba wa jami’an tsaro da shugabannin tsaro akan jajircewar su’, ranar Talata.

Shugaba Buhari ya yaba wa jami’an tsaro akan gudun-mawar da suke ba kasa

Kamar yadda The Punch ta ce, takardar ta bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba za mu lamunci garkuwa da mutane ba musamman na yara masu zuwa makaranta kuma zamu yi yaki da hakan. Ba za mu yarda da wani abu da zai kawo cikas ga harkokin ilimi da tattalin arziki ba.
“Mun bayar da umarni ga duk wasu jami’an tsaro don su kawo karshen halaka jama’a da dukiyoyi a kasar nan cikin gaggawa.
“Ina mai tabbatar muku da cewa mun tura jami’an tsaro duk fadin jihohin kasar nan don yaki da rashin tsaro.”

Kara karanta wannan

Bayan watanni 6, an gurfanar da wadanda ake zargi da hallaka yaron Sanata a gaban kotu

Ya bukaci ko wanne dan Najeriya ya taka tashi rawar wurin taimaka wa gwamnati don kawo karshen ta’addanci

Shugaban kasar ya kula da salon tsaron kasar nan na 2019 inda yace ya kawo gyara ga matsalar tsaro, don haka akwai bukatar jama’an gari, ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya su taimaka wa gwamnati wurin yaki da ta’addanci.

Shugaban kasar ya bukaci kowa ya nuna wa kasar sa kauna ta hanyar bayar da tashi gudun-mawar don tsaro ya inganta kuma yara su kubuta.

Ya ce wajibi ne a tallafa wa yara wadanda su ne manyan gobe don tsare su daga duk wata matsala da zata kawo wa rayuwar su cikas.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel