Da-Dumi-Dumi: Lamari ya ɗau zafi, Ministan Buhari ya fice daga dakin taro da Daliban Najeriya

Da-Dumi-Dumi: Lamari ya ɗau zafi, Ministan Buhari ya fice daga dakin taro da Daliban Najeriya

  • Kungiyar daliban Najeriya dake karatu a cikin ƙasa NANS ta mamaye harabar zauren majalisar tarayya da zanga-zanga
  • Wakilan daliban sun samu damar ganawa da ministan ilimi kan yajin aikin da ASUU ke yi, amma babu sakamako mai kyau
  • An hangi Ministan ya fice daga wurin taronsa da wakilan ɗaliban ba tare da cimma wata matsaya ba

Abuja - Ministan Ilimi na tarayyan Najeriya, Adamu Adamu, ya fice daga wurin tattauna wa da kungiyar daliban Najeriya (NANS) ba tare da cewa komai ba.

Channels tv ta rahoto cewa an karkare taro tsakanin bangarorin biyu ba tare da fitar da wata sanarwa game da abin da aka cimma wa ba.

Taro da Dalibai
Da-Dumi-Dumi: Lamari ya ɗau zafi, Ministan Buhari ya fice daga dakin taro da Daliban Najeriya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ministan ya gana da kungiyar NANS ne a wani yunkuri na kawo karshen zanga-zangar da ƴaƴan kungiyar suka fara a sassan Najeriya domin a janye yajin aiki.

Kara karanta wannan

Wani dankareren Maciji ya kusta kai Hostel din dalibai mata a Jami'a, sun yi ta kansu

Tun da farko dandazon ɗaliban suka mamaye kofar shiga zauren majalisar tarayya suna bukatar kawo karshen yajin aikin malaman jami'o'i.

'ASUU Must Go' daliban suka cigaba da rera wa yayin da suka durfafi babbar Kofar Unity Fountain ta shiga zauren majalisar tarayya.

Sai dai ɗaliban ba su sami yadda suke so ba na shiga zauren, kasancewar jami'an tsaro sun dakatar da su daga yunkurin su, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Abin da shugabannin ɗaliban suka faɗa

Shugaban NANS na ƙasa, Sunday Asefon, wanda ya jagoranci tawagar ɗaliban, ya ce kamata ya yi jami'an tsaron su shiga ayi zanga-zangar da su, saboda suna da ƴaƴa a jami'o'in Najeriya.

Ya kuma jaddada cewa kowane ɗan Najeriya na da yancin neman ilimi musamman matasa, kuma akwai bukatar FG da mambobin ASUU su sasanta kansu domin ɗalibai su koma makaranta.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Gwamnatin Buhari zata fara jigilar dawo da yan Najeriya da yaƙin Rasha-Ukraine ya rutsa da su

Ya ce:

"Ba mu zo dan mu tada hargitsi ba, abin da ya kawo shi ne mu gana da Ministan Ilimi."

Daga baya, an bai wa wakilan ɗaliban damar ganawa da Ministan Ilimi, amma sai taron ya ƙarkare ba tare da samun matsaya ba domin an hangi ministan ya fice daga wurin.

A wani labarin kuma Ana tsaka da yakin Rasha da Ukraine, Shugaba Buhari ya fice Najeriya ya nufi Turai

A ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ya dira Faris, babban birnin kasar Faransa, domin fara ziyarar aiki ta mako biyu.

A rahoton da TVC News ta tattaro, Jirgin shugaba Buhari ya ɗira a filin sauka da tashin jiragen sama na Le Bourget da misalin ƙarfe 7:45 na daren ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel