Rikici: Dan Najeriya ya rikice yayin da aka caje shi N1.7m maimakon N17k a gidan mai

Rikici: Dan Najeriya ya rikice yayin da aka caje shi N1.7m maimakon N17k a gidan mai

  • Shahararren mawakin nan na Najeriya, Speed Darlington, ya tafi shafin sada zumunta inda ya yi ta tofa albarkacin bakinsa kan abin da ya faru dashi a gidan mai
  • Tauraron mawakin ya bada labarin yadda yaje siyan man fetur na Naira 17,150 inda ma’aikacin gidan man ya caje shi Naira miliyan 1.7
  • Speed ya lura cewa ya saka lambar sa ba tare da ya bincika ba kuma ya zargi ma'aikacin da tafka kuskure saboda abokin ciniki ko yaushe shi ke da gaskiya

Shahararren mawakin nan na Najeriya, Speed Darlington, ya koka matuka a shafin sada zumunta bayan da ya yi kari a kudin man fetur da ya sha a wani gidan mai.

Tauraron mawakin a shafinsa na Instagram ya bayyana yadda yaje gidan mai siyan mai na Naira 17,150 amma ma’aikacin gidan man ya caje shi Naira miliyan 1.7.

Kara karanta wannan

Matar Aure Mai Ciki Ta Yi Garkuwa Da Kanta, Ta Siya Gida Da Kuɗin Fansar Da Ta Karɓa Daga Hannun Masoyinta Na Facebook

Kudin mai ya fita nesa da yadda ya saye
Rikici: Dan Najeriya ya rikice yayin da aka caje shi N1.7m maimakon N17k a gidan mai | Hoto: @speeddarlingtonoku
Asali: Instagram

Speed ya kara da cewa, ba tare da ya duba ko ya ga kuskuren ba, sai ya sanya lambobin sirrinsa kuma aka caje shi sama da miliyan.

Sai dai mawakin ya amince cewa an mayar masa da Naira miliyan 1.2 kuma yana kan hanyarsa ta komawa gare su domin karbar sauran.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, kawai ya iya babatu ta yanar gizo game da abin da ya faru ne saboda gidan man yana da nisa daga inda yake zaune.

A fadinsa:

“Ko da yake sun mayar mini da N1.2, ina kan hanyata ta zuwa karbo sauran. Amma za ku iya gaskata wannan kitimurmura? Na je siyan man fetur na Naira 17,150, mutumin nan ya yi kuskure ya cire Naira miliyan 1.7, na sa lambobin sirri na ba tare da na duba ba.
"Amma banga laifin kaina ba, ni kwastoma ne, kwastoma a ko yaushe yana da gaskiya, aikinsa ne ya yi daidai. Ina da bakin magana ne saboda yana kusa da ni, babu nisa dani, idan wannan ya faru a wata jihar ko ya zan yi?.”

Kara karanta wannan

Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba

Martanin 'yan soshiyal midiya

Mutane da dama sun yi martani kan wannan lamari, ga kadan daga martanin 'yan Instagram:

Posh.eve:

“Ka duba fa. Ka ga wasan banza oo."

Loyd_andriy:

"Kudin yakin neman zabe kenan."

Thelmatreasures:

"Kana ma da kudin ne. Idan na saya 1700 kuma aka danna 17k ba zai ma tafi ba."

Fine_olajide:

“Ba ma 170k ba, 1.7m. Walahi kotu zan kaisu kai tsaye."

Saurayi ya fusata ya garzaya Kotu bayan gano budurwarsa ta siyar da dansu na kafin Aure

A wani labarin, wani bawan Allah musulmi da ya yi nufin rada wa dan da suka haifa da budurwarsa Kirista, Justina Yakubu, sunan addinin musulunci ya shigar da kara Kotu.

Punch ta rahoto cewa Saurayin ya maka budurwarsa a Kotu ne bayan gano cewa ta batar masa da dan da suka haifa kafin aure, duk da suna shirin auren juna.

Suleiman Ibrahim, ya bayyana cewa ya fada kogin soyayya da Justina Yakubu, mai bin addinin Kirista, kuma ta masa alkawarin zata aure shi.

Kara karanta wannan

Ba A Fahimci Ni Bane Da Na Ce ‘Na Shirya Ƙazamin Artabu Da Kowa’, Tinubu Ya Yi Ƙarin Haske

Asali: Legit.ng

Online view pixel