Rikita-Rikita: Saurayi ya fusata ya garzaya Kotu bayan gano budurwarsa ta siyar da ɗansu na kafin Aure

Rikita-Rikita: Saurayi ya fusata ya garzaya Kotu bayan gano budurwarsa ta siyar da ɗansu na kafin Aure

  • Wani Saurayi Musulmi ya garzaya neman hakkinsa kan budurwar da yake son aure Kirista, bisa zargin ta siyar da ɗan su na kafin aure
  • Suleiman ya bayyana cewa sun sha soyayya da Justina Yakubu, bisa alkawarin za su yi aure har Allah ya ba su ɗa guda ɗaya
  • Yan sanda sun gano cewa Justina ta sayar da jaririn kan kudi Naira N120,000, kuma ta masa laifinta a Kotu

Adamawa - Wani bawan Allah musulmi da ya yi nufin raɗa wa ɗan da suka haifa da budurwarsa Kirista, Justina Yakubu, sunan addinin musulunci ya shigar da ƙara Kotu.

Punch ta rahoto cewa Saurayin ya maka budurwarsa a Kotu ne bayan gano cewa ta batar masa da ɗan da suka haifa kafin aure, duk da suna shirin auren juna.

Kara karanta wannan

Rikita-Rikita: Wani mutumi da aka ce ya mutu ya dawo gida bayan shekara 5, Matarsa ta guje shi

Suleiman Ibrahim, ya bayyana cewa ya faɗa kogin soyayya da Justina Yakubu, mai bin addinin Kirista, kuma ta masa alkawarin zata aure shi.

Jihar Adamawa
Rikita-Rikita: Saurayi ya fusata ya garzaya Kotu bayan gano budurwarsa ta siyar da ɗansu na kafin Aure Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace daga nan soyayya mai karfi ta kullu a tsakanin su, suka cigaba da shagalinsu kuma Allah ya albarkace su da samun haihuwa tun kafin aure.

Ya ƙara da cewa bayan ta sauka lafiya, ya sanar da Justina cewa zai raɗa wa ɗan suna kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, kuma ya sake tuna mata alkawarin auren su.

Bayan haƙa ne, budurwar ta sa da yake da niyyar aure ta shaida masa cewa jaririn ya bata batasan inda ya yi ba.

Rahotanni sun nuna cewa Suleiman bai amince da bayanin masoyiyar budurwarsa ba, hakan ya sa ya garzaya kai korafinta wurin yan sanda.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Yan sanda suka kame Justina tare da wata mai shayarwa, Esther Romanus, wacce ake zargin ta sayi jaririn kan kudi N120,000.

Mahifin yaron ya ce Justina ta karbi N20,000 daga cikin kuɗin, ta biyo bashin ragowar N100,000 hannun wace ta siya.

Hukumar yan sanda ta gurfanar da matan biyu a gaban Kotun Majistire dake Yola. Justina ta amsa laifinta amma matar ta ce sam ba da ita aka haɗa wannan cinikin ba.

Mai gabatar da kara daga hukumar yan sanda, Sajan Sawe Nicholas, ya shaida wa Kotu cewa:

"Mahaifin jaririn, Sulaiman ne ya kawo rahoto abin da ya faru ranar 2 ga watan Fabrairu. Ya shaida mana Justina ta gudu da ɗan su, Jamilu, daga baya tace masa ya ɓace."
"Bayanan da muka samu na farkon bincike sun nuna cewa ta haɗa kai da wata mata sun siyar da yaron."

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Kara karanta wannan

Amarya ta daba wa Uwar gida wuka har lahira mintuna kaɗan bayan Jima'i da Maigida

Bayan sauraron kowane bangare, Mai shari'a Abdullahi Digil, ya ɗage sauraron karar zuwa 25 ga watan Fabrairu, 2022, domin baiwa yan sanda damar kammala bincike.

A wani labarin kuma Majalisar Dokoki ta tsige mataimakin kakaki, yan majalisu biyu sun sauya sheka zuwa APC

Majalisar dokokin jihar Ebonyi ta bayyana murabus ɗin mataimakin kakaki da wasu mambobinta biyu a zaman Litinin.

Sai dai lamarin ya tada hatsaniya, yayin da mutanen uku baki ɗaya suka musanta ikirarin majalisa, suna nan daram a matsayin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel