Gwamnan Bauchi ya amince da naɗin Nuhu Wabi matsayin sabon sarkin Jama'are

Gwamnan Bauchi ya amince da naɗin Nuhu Wabi matsayin sabon sarkin Jama'are

  • Gwamnan Bauchi, Bala Muhammed ya nada Alhaji Nuhu Ahmed Wabi a matsayin sabon sarkin Jama'are ta jihar Bauchi
  • An mika wa sabon sarkin takardar kama aiki ne bayan tantancewar da masu nadin sarauta na masarautar Jama'are suka yi
  • Gwamnan da ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, ya bukaci Sarkin da ya dage wurin sauke nauyin da aka dora masa na jama'a

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed ya amince da nadin Alhaji Nuhu Ahmed Wabi a matsayin sabon sarkin Jama'are.

Gwamnan ya bayyana amincewarsa ne a wani karamin biki a Jama'are, Bauchi a ranar Litinin inda sabon sarkin ya karba takardar kama aiki, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan Bauchi ya amince da naɗin Nuhu Wabi matsayin sabon sarkin Jama'are
Gwamnan Bauchi ya amince da naɗin Nuhu Wabi matsayin sabon sarkin Jama'are. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Bala ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Barista Ibrahim Kashim, Daily Trust ta ruwaito.

Nadin Nuhu Wabi ya bayyana bayan sati uku da mutuwar mahaifinsa, Alhaji Ahmadu Muhammadu Wabi, wanda ya rasu a ranar 5 ga watan Fabrairu. Ya yi shekaru 52 yana mulki.

Kara karanta wannan

Masarautar Kano ta baiwa kamfanin Air Peace kwanaki 3 ta baiwa Sarkin Kano hakuri

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Bala ya ce nadin Nuhu Wabi ya biyo bayan duba sunayen da aka mika wa masu nada sarakunan masarautar Jama'are.

Ya taya sabon sarkin murna kuma ya yi kira gare shi da ya sauke nauyin da aka dora masa na mutanensa.

Sabon sarkin ya yi alkawarin tabbatar da alakar aiki mai kyau tsakaninsa da sauran masarautu a jihar.

Nuhu Wabi shi ne babban dan marigayin basaraken. Har zuwa lokacin da aka nada shi sarki, Alhaji Wabi shi ne yariman Jama'are mai jiran gado.

Sabon sarkin an haife shi a Jama'are a shekarar 1961. Ya halarci Jama’are Central Primary School, makarantar sakandaren gwamnati da ke Kuranga a Azare da kuma jami'ar jihar Jos.

Sabon sarkin ya yi aiki da ma'aikatar ayyuka ta tarayya na tsawon shekara hudu kafin ya koma ma'aikatar gwamnatin jihar Bauchi a matsayin jami'i.

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

Ya yi ritaya a shekarar 2013 a matsayin babban sakataren gwamnati.

Innalillahi: Sarkin Jama'are, Dakta Ahmadu Muhammad Wabi ya riga mu gidan gaskiya

A wani labari na daban, daga Allah mu ke, gare shi za mu koma. Ubangiji mai kowa mai komai ya dauka rayuwar Mai Martaba Sarkin Jama'are ta jihar Bauchi, Alhaji dakta Ahmadu Muhammad Wabi III.

Basaraken ya rasu wurin karfe 12 na daren Asabar wacce za ta sada mu da ranar Lahadi, shida ga watan Fabrairu kamar yadda Gado da Masun Jama'are, Alhaji saleh Malle ya sanar da BBC.

Dakta Ahmadu Wabi ya koma ga mahaliccin sa ne bayan fama da rashin lafiyar da yayi. Basaraken da ya shafe kimanin shekaru hamsin a kan karagar mulkin Jama'are, ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya 35 da jikoki masu yawa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel