Masarautar Kano ta baiwa kamfanin Air Peace kwanaki 3 ta baiwa Sarkin Kano Hakuri

Masarautar Kano ta baiwa kamfanin Air Peace kwanaki 3 ta baiwa Sarkin Kano Hakuri

Shugaban tsare-tsare na masarautar Kano, Isah Bayero, ya baiwa Air Peace sa'o'i 72 su baiwa mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, hakuri bisa wulakantashi da suka yi da jinkirta tafiyarsa.

Malam Isah Bayero ya bayyana hakan ranar Asabar yayin hira da wasu manema labarai a jihar Kano, rahoton Premium Times.

Sarkin Kano
Masarautar Kano ta baiwa kamfanin Air Peace kwanaki 3 ta baiwa Sarkin Kano Hakuri Hoto: Sarkin Kano
Asali: Facebook

Yace wajibi ne kamfanin Air Peace ya amsa cewa yayi laifi wajen kin bin tsari, wanda haka ya sabbaba jinkirin Sarkin Kano a tashar jirgin Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Tunda mun yi jinkirin barin Banjul da awa guda, ya kamata su sani da akwai fasinjoji goma dake niyyar zuwa Kano kuma suyi abinda ya kamata saboda ba laifinmu bane jinkirin da ya faru."

Kara karanta wannan

Air Peace vs Sarkin Kano: Muna baiwa kwastmominmu hakuri amma ba laifinmu bane

"Na kirasu sau da dama amma suka ki daukan waya sai daga baya sukace ba zai yiwu ba.Ya kamata shugabannin kamfanin su rika yiwa manyan mutane shiri na musamman."
"Tun da sun jinkirta tashinmu daga Banjul, wanda ya sabbaba jinkirin zuwa Legas, ya kamata Air Peace ya shirya yadda za'a damu. Amma babu abinda sukayi."
"Ina basu sa'o'i 72 su baiwa Sarki hakuri, na farko a jarida, na biyu kuma su turo wakilai wajen Sarki. Babu abinda ba zamu iya yi don kare mutunci masarautarmu ba."

Air Peace ya ‘ci mutuncin’ Sarki Aminu Ado Bayero da tawagarsa a filin jirgi, Fadar Kano

Da farko Isah Bayero ya rubuta takardar korafi zuwa ga hukumar NCAA ta tarayya.

Daily Trust ta ce Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot ne ya aika wasika ga NCAA a kan abin da ya kira cin mutunci da aka yi wa Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin Masarautar Kano da Kamfanin jirgi: Ya kamata manya su saka baki, inji wata kungiya

Isa Sanusi Bayero ya zargi kamfanin jirgin Air Peace da cin zarafin Sarki da mutanen kasar Kano.

Ta wani dalili zamu jinkirta jirgin da ya fara tafiya saboda mutum 1, Air Peace ya yi raddi

Kamfanin jirgin sama na Air Peace, ya bayyana cewa ko kadan bai ci mutuncin mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ba.

Shugabar harkokin ayyyukan kamfanin, Toyin Olajide, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa karya Isa Bayero ya sharara saboda kamfanin Air Peace na ganin girman Sarkin Kano matuka.

A cewarta, sabanin abinda ake yadawa na cewa kamfanin ya ci mutuncin Sarkin, kare mutuncin Sarkin akayi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel