Yakin Rasha da Ukraine: Za a cigaba da karancin man fetur a Najeriya

Yakin Rasha da Ukraine: Za a cigaba da karancin man fetur a Najeriya

Akwai yuwuwar yakin da ake fafatawa tsakanin Russia da Ukraine zai tsawaita karancin man fetur din da ake fuskanta fiye da makonni uku da suka wuce, alamu sun nuna yawancin kayayyakin da matata ke samarwa da ake shigowa dasu cikin Najeriya, daga sasannin da ake yakin zasu fuskanci jinkiri.

An tattaro a ranar Lahadi, cewa 'yan kasuwan dake siyarwa Najeriya kayyayakin da ake samarwa daga man fetur zasu iya samun tsaiko, saboda raguwar da aka samu na jiragen Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC).

Yakin Rasha da Ukraine: Za a cigaba da karancin man fetur a Najeriya
Yakin Rasha da Ukraine: Za a cigaba da karancin man fetur a Najeriya. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

NNPC tana shigo da tataccen man fetur cikin Najeriya, daga 'yan kwangila da 'yan kasuwa ta hanyar tsarin siyarwa da saye kai tsaye, The punch ta ruwaito

Tabbattatun majiyoyi daga masu harkar mai da sauran 'yan kasuwa sun bayyana a ranar Lahadi yadda Najeriya da NNPC ta samu raguwa na kimanin jiragen 17 a DSDP din ta, saboda raguwar samar da man fetur.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: 'Yan Najeriya sun samu mafaka a kasashe biyu da ke makwabtaka da Ukraine

Sun ce, hakan ka iya tsawaita karancin man fetur din da ake fama dashi a fadin kasar, sai dai idan an yi amfani da matakin rashin dakatar da gudanarwar bangarorin man fetur.

Sun kara da bayyana yadda yakin Rasha da Ukraine ka iya assasa matsalar man fetur a Najeriya, saboda yadda za a iya tsaida abubuwan da ake samarwa daga man daga barin matatar.

The punch ta ruwaito cewa, a halin yanzu, an dakatar da shigowa da abubuwan da ake samarwa daga man fetur cikin Najeriya.

"Za mu iya siffanta abunda muke fuskanta a halin yanzu a matsayin annoba, wanda ke aukuwa idan abubuwa da dama basu tafiya yadda ya kamata a lokaci daya. Muna fuskantar matsaloli, amma wannan matsalar tana faruwa ne a lokacin da wata matsalar ta faru, hakan yasa komai ya hargitse," Wani mai kasuwancin man fetur da NNPC, wanda ya bukaci a sakaya sunan sa saboda tsaro ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Garin dadi na nesa: Bidiyon gidan mai a Dubai da ake yawo da shi ya janyo cece-kuce

Majiyar ta kara da cewa, "Yanzu da kasar Rasha ta kaiwa Ukraine hari. Menene mahadin harin da Rasha ta kaiwa Ukraine ga Najeriya? Rasha kasa ce dake samar da man fetur, ita kuma Ukraine ke tace mana kayan da aka tato daga mai a fadin duniya, ba gabashin Europe kadai ba.
"Hakan yasa farashi ya daga, saboda tatattun kayayyakin suna zuwa ne daga wannan sassan duniya, kuma tashin hankali irin wannan zai zamo tangarda ga samar da kayyakin."
Har ila yau majiyar ta kara da, "A kullum OPEC tana neman gangunan mai 1.7 miliyan daga Najeriya, amma abunda take iya samar wa yana tsakanin 1.3 zuwa 1.4 miliyan na gangunan man fetur a kullum. Amma wannan wani abu ne daban. Yanzu daga 1.3 miliyan na gangunan man da kasar ke samar wa a kullum, mutane na sata daga shi.
"Su na yin ramuka a jikin magudanar man, inda ake amfani da man da suka sata a matatun da ba a yarda dasu ba a jihar Rivers, hakan ke sanya cuta da matsalar huhun mutane. Sauran wadanda suka sace, suna sawa a ababen hawa don siyarwa a manyan kasashe," yace.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu

Tsadar mai: Bidiyo ya fallasa yadda ake sayar da gurbataccen mai a wani gidan mai

A wani labari na daban, yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa ta kowane bangare, wasu masu gidajen mai suna kara wa ciwon gishiri ta hanyar sayar da gurbataccen mai.

Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya bayyana lokacin da wani ma'aikacin gidan mai ke kokarin cika wata gorar ruwa da wani mai launin ja da ya yi kama da gurbatacce.

A bidiyon da Legit.ng Hausa ta samo a kan shafin Facebook na jaridar Punch, an ga man da ake dura wa gorar da launin da bai yi kama da na man fetur ko kalanzir ko gas ba, duk da cewa a gidan mai ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel