Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Buhari zata fara jigilar dawo da yan Najeriya gida daga Ukraine

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Buhari zata fara jigilar dawo da yan Najeriya gida daga Ukraine

  • Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala shirye-shirye kuma tana fatan fara debo yan Najeeiya da rikicin Rasha-Ukraine ya rutsa da su
  • Ministan harkokin kasashen waje, Onyeama shi ne ya bayyana haka yayin ganawa da kakakin majalisar dokokin tarayya
  • Haka nan Ministan ya musanta rahoton dake yawo cewa ana nuna wa bakaken fata wariyar launi idan suka je wucewa ta iyakar ƙasa

Abuja - Gwamnatin tarayya zata fara jigilar dawo da yan Najeriya da suka maƙale a rikicin Rasha da Ukraine gida.

Ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, shi ne ya bayyana haka yayin ganawa da kakakin majalisar dokokin tarayya, Femi Gbajabiamila, ranar Litinin.

A wani sako da kakakin ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce gwamnati zata fara aikin dawo da yan ƙasarta gida Najeriya ranar Laraba.

Taron Minista da Kakakin majalisa
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Buhari zata fara jigilar dawo da yan Najeriya gida daga Ukraine Hoto: @Speakergbaja
Asali: Twitter

Ministan ya ce Najeriya ta kammala duk wasu shirye-shiryen dawo da yan ƙasa gida, waɗan da suka keta zuwa wasu ƙasashen saboda yaƙin Rasha-Ukraine.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Muna fatan fara jigilar dawo da su gida ranar Laraba, muna aiki ba dare da rana dan tabbatar da ranar Laraba mai zuwa mun tura jirgi ya debo su."

Shin dagaske ne ana nuna wa yan Najeriya wariya?

Haka nan kuma, Mista Onyeama, ya musanta raɗe-raɗin cewa ana nuna wa baƙaƙaen fata yan Najeriya wariyar launin fata idan suka zo keta iyaka zuwa wata ƙasa daga Ukraine.

Ya ƙara da cewa:

"Shawarar da muka bayar a baya ta ƙara wa yan Najeriya kwarin guiwa, amma daga sanda aka fara kai farmaki ta sama, dandazon mutane suka fara tunkarar iyaka."
"Kuma lokacin da na fara jin labaran nuna wariyar launin fata da banbamci, na kira Ministan Ukraine, kuma ya shaida mun lamarin ba shi da alaƙa da tsren ceton yan ƙasa."

A wani labarin na daban kuma Ana tsaka da yakin Rasha da Ukraine, Shugaba Buhari ya fice Najeriya, ya nufi Turai

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai halarci taron zaman lafiya a Farisa, wanda aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris.

Domin samun halartar taron na duniya, shugaban ƙasa ya bar fadarsa Aso Villa ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel