Atiku Abubakar ya ajiye siyasa, ya ba Buhari shawara a kan rikicin Rasha v Ukraine

Atiku Abubakar ya ajiye siyasa, ya ba Buhari shawara a kan rikicin Rasha v Ukraine

  • Atiku Abubakar ya tsoma baki a game da mummuan yakin da yake neman ya barke yanzu a Duniya
  • ‘Dan siyasar na Najeriya ya ba kasashen Duniya shawarar yadda za su bi domin su magance rikicin
  • Atiku wanda ya dade yana harin kujerar shugaban kasa ya nemi a dauke ‘Yan Najeriya da ke Kyiv

A ranar Alhamis 24 ga watan Fubrairu, 2022, Atiku Abubakar ya yi magana a game da yakin da barke yanzu haka tsakanin Ukraine da kuma Rasha.

Kamar yadda mu ka fahimta daga shafinsa na Twitter, Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauko ‘yan Najeriya da ke zaune a Ukraine.

Tsohon ‘dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa mafi yawan mutanen Najeriya da suke Ukraine, dalibai ne don haka ake bukatar a dauko su.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga

Atiku Abubakar wanda ya kan fito ya yi jawabi irin wannan, ya yi kira ga Muhammadu Buhari da sauran kasashen Duniya su yi amfani da hanyar lalama.

‘Dan siyasar yana ganin cewa ta hanyar yin sulhu ne za a iya magance wannan yaki da ake yi.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar Hoto: Atiku
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Rikicin Rasha da Ukraine yana bukatar duka kasashen Duniya su tashi tsaye, su bi ta hanyar neman sasanci domin shawo kan lamarin.”
“Ina kuma rokon gwamnatin Najeriya tayi duk abin da za ta iya domin a dauke mutanen Najeriya da ke Ukraine, mafi yawansu duk ‘dalibai ne.”

Abin da mutane su ke fada:

Yanzu haka ina birnin Kyiv, kasar Ukraine. Mu na barar addu’o'i a wannan lokaci.

- Udo Toi

“Idan da a ce gwamnati ta na daukar dawainiyar jami’o’inmu, da babu dalilin su tafi karatu a can. Idan ka samu mulki, ka yi bakin kokarinka…”

Kara karanta wannan

Rasha ta fara kai hare-hare a Ukraine, ‘Daliban Najeriya 4, 000 sun yi carko-carko

- Aeekh

Gwamnatin Najeriya da ta gaza ceto ran mutanen da ake ta kashewa, ana garkuwa su, ita ake sa ran za ta je wata kasa a ketare, ta dauko ‘Yan Najeriya

- En Jay Smooth

Asali: Legit.ng

Online view pixel