Saudiyya za ta ci tarar SAR 2000 kan duk wanda ya kunna waka yayin kiran sallah a kasar

Saudiyya za ta ci tarar SAR 2000 kan duk wanda ya kunna waka yayin kiran sallah a kasar

  • Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta saka tarar SAR 2000 kan wadanda ke kunna wakoki yayin da ake kiran sallah a kasar
  • Har ila yau, daga cikin sabbin dokoin da kasar ta sanyawa 'yan kasa da mahajjata, akwai hana zuwa masallatai da gajerun wanduna
  • Gwamnatin kasar Saudiyyan ta sanar da cewa hatta makwabci idan ya kai karar makwabci kan damunsa da waka, za a ci tararsa

Saudi Arabia - Gwamnatin Saudi Arabia sun kara gyara dokoki ga mahajjata a Makkah da Madinah ta hanyar samar da sabbin matakai, wanda aka gabatar wa al'umma a ranar Asabar.

Kamar yadda gwamnatin ta fada, mahajjatan da suke tahowa daga masarautar ko daga sauran kasashe, ana ganin su na amfani da ababen hawa yayin kiran sallah ( Adhan), wanda hakan bai dace ba, kuma haramun ne, The Islamic Information ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame magidanci a gidan yari bayan ya kara aure babu sanin uwargidansa

Saudiyya za ta ci tarar SAR 2000 kan duk wanda ya kunna waka yayin kiran sallah a kasar
Saudiyya za ta ci tarar SAR 2000 kan duk wanda ya kunna waka yayin kiran sallah a kasar. Hoto daga @haramainsharifain
Asali: Twitter

Saboda haka ne, hukumomin Saudi suke jan kunnen al'umma a kan wasa ko kara sautin waka a cikin gidajen dake anguwanni yayin Adhan da Iqamah ( kiran sallah na farko da na biyu).

Daga yanzu duk wanda aka kama ya kunna kowanne irin waka yayin da masallatai suke kiran sallah za a ci shi tarar Riyal 1000 idan wannan shine karonshi na farko, amma idan ya sake, za a ci shi taran Riyal 2000 saboda sake karya doka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yana da mahimmanci a tuna cewa, tarar za ta zama wajibi ne idan an kure sautin wakar yayin da ake kiran sallah a masallaci. Sannan dokar ta hada da wadanda ke kure sautin wakar a motoci da gidajensu. Sannan, dokar ba ta shafi masu sauraran wakoki a sifikar kunne ba.

Bugu da kari, Saudi Arabia ta wajabta tarar Riyal 500 ga duk wanda ya kure sautin waka a gida ga makwabci, idan makwabcin ya kai kara.

Kara karanta wannan

Bai hallata mace 'yar sanda ta dau juna biyu ba muddin ba tada aure, Kotu ta yanke

Gwamnatin Saudi Arabia ta gabatar da sabuwar tara daga Riyal 250 zuwa Riyal 500 ga duk wanda ya sanya gajeren wando zuwa masallaci ko ofishoshin gwamnati.

Za a fitar gami da cin shi tarar Riyal 500 ga duk wanda ya shiga masallatan biyu da gajeren wando, The Islamic Information ta tabbatar.

A cewar ma'akatan, sanya gajerun wanduna a masallatai da ma'aikatun gwamnatin bayan tabbatar da sabuwar dokar ya sabawa ladubban zamani.

Sai dai, gwamnatin ta yi fashin baki ga maza masu sanya gajerun wanduna a cikin anguwanni, da cewa ba za a dauki hakan a matsayin karya doka ba, sai dai a masallatai.

An gabatar da sabuwar tarar ne, jim kadan bayan ministan walwala na Saudi, Prince Abdulaziz Bin Saud Bin Naif ya gabatar da sabuwar dokar dake kira ga canjin tsarin dokoki.

Hajji da Umrah: Kasar Saudi Arabia za ta dage takunkumi kan jiragen Najeriya, Jakada

A wani labari na daban, Saudi Arabia ta ce za ta dage dokar da ta kafa ta dakatar da jiragen sama daga Najeriya zuwa kasar don bai wa masu niyyar zuwa Hajji damar yin bautar.

Kara karanta wannan

Neja: An sha yar dirama yayin da kansila ya fatattaki jami’an gwamnati da karnuka da yan daba

Jakaden Saudiyya a Najeriya, Mr Faisal Bin Ibraheem Al-Ghamidy ne ya sanar da hukumar hajji ta kasar Najeriya, NAHCON a lokacin da ta kai masa ziyara ofishin sa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

A watan Disamban 2021 ne Saudiyya ta sanar da dokar dakatar da jiragen sama daga Najeriya zuwa Saudiyya a kan yaduwar sabuwar nau’in cutar COVID-19.

Asali: Legit.ng

Online view pixel