Gwamnatin Buhari ta jero iyakoki 4 da 'yan Najeriya za su bi su fita daga Ukraine

Gwamnatin Buhari ta jero iyakoki 4 da 'yan Najeriya za su bi su fita daga Ukraine

  • Gwamnatin Najeriya ta amsa kiraye-kirayen da mutane ke yi yayin da ta aika bayanan da za su taimaka wajen kare yan kasarta da suka makale a kasar Ukraine
  • Gwamnatin ta hannun shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri, ta lissafa iyakokin da yan Najeriya za su bi su fita daga Ukraine
  • Ofishin Jakadancin Najeriya a Warsaw, kasar Poland ya sanar tun farko cewa jami’ai da yan sa-kai za su kasance a kan iyakokin Poland da Ukraine domin daukar ‘yan Najeriya

A ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu, gwamnatin tarayya ta lissafa iyakokin da yan Najeriya da ke tserewa daga yakin Ukraine da Rasha za su iya bi zuwa Poland.

Dakarun sojojin Rasha sun mamaye babbar birnin Ukraine, Kyiv, sannan an kashe mutane da dama tun bayan da aka fara yakin.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya ajiye siyasa, ya ba Buhari shawara a kan rikicin Rasha v Ukraine

Abike Dabire-Erewa, shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna waje, ta bayyana hakan sannan ta sanar da iyakokin da ya kamata yan Najeriya da ke guje ma yakin su bi, Daily Trust ta rahoto.

Gwamnatin Buhari ta jero iyakokin da 'yan Najeriya za su bi su fita daga Ukraine
Gwamnatin Buhari ta jero iyakokin da 'yan Najeriya za su bi su fita daga Ukraine Hoto: Pierre Crom/Getty Images
Asali: Getty Images

Iyakokin sun hada da:

1. Hrebenne-Rawa Ruska,

2. Korczowa-Krawkowiec,

3. Medyka-Szeginie,

4. Budomierz-Hurszew.

Abike ta bayar da tabbacin cewa:

“Kungiyoyin sa-kai na Najeriya, da ma’aikatan ofishin jakadancin Najeriya, za su kasance a iyakar domin kwashe yan Najeriya.”

An Kama Dakarun Sojojin Rasha a Ukraine

A wani labarin, mun ji cewa yayin da ake tafka fada tsakanin Rasha da Ukraine, dakarun sojojin Ukraine sun kama wasu sojojin Rasha.

Tawagar tattara bayanan sirri, CIT, wasu masu bincike a Rasha da Ukraine sun tabbatar da kama sojojin na Rasha, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata kwaso yan Najeriya dake zaune a kasar Ukraniya

CIT ta wallafa hotunan sojojin a shafinta na Twitter, tare da nuna makamai da aka ce an kama sojojin da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel