Labari Da Duminsa: An Kama Dakarun Sojojin Rasha a Ukraine

Labari Da Duminsa: An Kama Dakarun Sojojin Rasha a Ukraine

  • Dakarun kasar Ukraine sun kama wasu sojojin Rasha hudu dauke da bindigu, harsashi da wuka a wani yanki na Rasha
  • A wani bidiyo da ake musu tambayoyi daya daga cikin sojojin da aka kama ya ce tilasta shi aka yi bai yi niyyar zuwa ba
  • Shugabannin kasashen duniya da majalisar dinkin duniya sun yi Allah wadai da kutsen da Rasha ta fara yi wa Ukraine

A yayin da ake tafka fada tsakanin Rasha da Ukraine, dakarun sojojin Ukraine sun kama wasu sojojin Rasha.

Tawagar tattara bayanan sirri, CIT, wasu masu bincike a Rasha da Ukraine sun tabbatar da kama sojojin na Rasha, Daily Trust ta rahoto.

CIT ta wallafa hotunan sojojin a shafinta na Twitter, tare da nuna makamai da aka ce an kama sojojin da su.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Labari Da Duminsa: An Kama Sojojin Sojojin Rasha a Ukraine
An Kama Sojojin Sojojin Rasha a Ukraine. Hoto: AFP/Getty Images
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce an kama sojojin na Rasha ne da tankunan yaki a yankin Belgorod a Rasha kafin kutsen da Rasha ta yi a ranar Alhamis, aka gano su a wajen Kharkiv, Daily Trust ta ruwaito.

An rahoto cewa suna dauke da harsasai da wukake da bindigu.

"Jami'in watsa labarai na sojojin Ukraine, Anatoliy Shtefan ya wallafa hotunan abin da ya yi kama da sojojin Rashan da aka kama," a cewar rubutun da ke tare da hoton kamar yadda Google ta fassara.

Ma'aikatar harkokin kasashen waje na Ukraine ta tabbatar da kama sojojin na Rasha

Jami'in watsa labarai na ma'aikaar harkokin kasashe waje na Ukraine, Oleg Nikolenko, shima ya tabbatar da hotunan sojojin.

Babban kwamandan sojojin Ukraine Valeriy Zaluzhny: 'Sojojin Ukraine sun kama fursunoni, sojojin Rasha biyu na tawagar 91701 na Yampol,' Nikolenko ya wallafa a Twitter.

Kara karanta wannan

Dakarun Rasha sun hallaka Sojojinmu 137 daga fara yaki inji Shugaban kasar Ukraine

Ya jadada cewa Rasha na shan kaye sakamakon kutsen da ta yi.

"Makiya na shan kaye. An kona tankokin Rasha hudu a Kharkiv ring road," ya wallafa a Twitter.

Wani bidiyo ya fito da ke nuna sojojin da aka kama yayin da ake musu tambayoyi.

Olexander Scherba, jakadan Ukraine a kasar Austria daga 2014 zuwa 2021, ya wallafa bidiyon a Twitter.

Wani bidiyo ya fito da ke nuna sojojin da aka kama yayin da ake musu tambayoyi.

Olexander Scherba, jakadan Ukraine a kasar Austria daga 2014 zuwa 2021, ya wallafa bidiyon a Twitter.

An ji daya daga cikin sojojin da aka umurta ya aika wa iyayensa sako yana cewa, "Mama, Baba, ban yi niyyar zuwa ba. Tilasta ni aka yi."

Kasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine.

A wani atisayen daban, sojojin Ukraine sun kama sojojin Rasha sun yi holen su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel