Da Dum-Dumi: Zamu kara korar malaman makaranta a Kaduna, Gwamna El-Rufa'i

Da Dum-Dumi: Zamu kara korar malaman makaranta a Kaduna, Gwamna El-Rufa'i

  • Gwamnatin Kaduna zata kara sallaman malaman makarantun Sakandire da ba su cancanci koyarwa ba a shekarar 2022
  • Gwamna El-Rufa'i ne ya tabbatar da haka, ya ce gwamnatinsa ta ɗauki ma'aikata sama da 40,000 cikin shekara 5 da suka gabata
  • Ya ce burinsa shi ne ya gyara ingancin karatun makarantun gwamnati ta yadda zai iya saka ɗansa ya yi karatu

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya ce gwamnatinsa zata kara sallamar malaman Makarantun Sakandire da basu cancanta ba a cikin 2022.

Punch ta rahoto Malam El-Rufa'i ya koka kan cewa wasu malaman takardar Firamare kaɗai gare su, amma an ɗauke su suna koyarwa a makarantun Sakandire na gwamnati.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis da safe a wurin taron manema labarai na Ministoci da ake gudanarwa mako-mako, wanda tawagar yan Midiya na fadar shugaban ƙasa ke shiryawa

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Gwamnan Kaduna, Mal Nasiru
Da Dum-Dumi: Zamu kara korar malaman makaranta a Kaduna, Gwamna El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i/Facebook
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki ma'aikata fiye da adadin yawan waɗan da ta sallama daga bakin aiki a shekaru biyar da suka gabata.

El-Rufa'i ya ce:

"Mun ɗauki ma'aikata sama da 40,000 a shekaru biyar da suka gabata, mafi yawancin su ma'aikatan jinya ne, Unguwan Zoma da malaman makaranta."

Bugu da ƙari, Malam El-Rufa'i yace a yanzu da yake jawabi, gwamnatinsa ta ɗauki sabbin malaman Sakandire 7,700 da suka cancanta aiki a faɗin jihar.

A cewarsa da zaran an kammala bankaɗo waɗan da takardun karatun su bai kai su koyar a Sakandire ba, za'a tura sabbin da aka ɗauka zuwa Makarantun Sakandiren dake faɗin Kaduna.

Menene maƙasudin da yasa gwamnatin Kaduna ke haka?

Tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja, yace babban burinsa shi ne ya gyara sashin ilimi a makarantun gwamnatin Kaduna domin 'ya'yan talakawa su sami ingantaccen ilimi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Dira Lafia, Babban Birnin Jihar Nasarawa

A cewarsa, fatan da yake makarantun su gyaru, su zama waɗan da za'ai gogayya da su, kuma su kai matakin da zai iya sanya ɗansa ya yi karatu a ciki.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da ya sanya ɗansa a makarantar gwamnati, amma ya cire shi saboda barazanar garkuwa, wanda ka iya jefa 'ya'yan talakawa a hatsari.

A wani labarin kuma Daruruwan mambobi a mahaifar dan takarar gwamna na PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Yayin da zaben 18 ga watan Yuni na gwamnan jihar Ekiti ke kara matsowa, jam'iyyar APC ta yi sabbin mambobi a Efon Alaye.

Dandazon mambobin PDP a garin da dan takarar jam'iyyar ya fito, sun sauya sheka zuwa APC mai mulkin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel