Tsohon Mai ba APC shawara ya cire Tinubu, Osinbajo daga lissafin 2023 saboda abu 2

Tsohon Mai ba APC shawara ya cire Tinubu, Osinbajo daga lissafin 2023 saboda abu 2

  • Dr. Muiz Banire SAN ya na goyon bayan a kai takara zuwa kudu maso gabashin Najeriya a 2023
  • Banire ya na kuma ganin Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu duk sun yi tsufa da hawa mulki
  • Kwararren lauyan ya taba rike kujerar babban Mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkokin shari’a

Abuja - Tsohon mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkar shari’a, Dr. Muiz Banire ya yi waje da Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu daga takara a zaben 2023.

Da aka yi wata hira da shi a gidan rediyon nan na RadioNow, Dr. Muiz Banire ya yi magana game da siyasar Najeriya, ya ce bai san da shirin takarar Bola Tinubu ba.

Daily Trust ta rahoto Muiz Banire wanda ya yi kwamishina a karkashin gwamnatin Asiwaju Bola Tinubu yana cewa kudu maso gabas ya kamata a kai mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Buhari ya tsaida wanda yake so ya zama sabon Shugaban Jam’iyyar APC

“Bayan bayyana manufarsa da ya yi a fadar Aso Villa, inda ya ce ya zo sanar da shugaban kasa, kuma yana tattaunawa da mutane, ban da labarin ya na takara.”

- Muiz Banire

Banire ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Legas yana da damar da zai nemi shugabanci, amma a ra’ayinsa zai fi so a ce mai kananan shekaru ya samu mulki.

Tinubu da Osinbajo
Farfesa Yemi Osinbajo da Asiwaju Bola Tinubu Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

“Mu na bukatar mutane, amma idan ka tambaye ni, zan fi goyon bayan masu kananan shekaru. Na fi son wadanda ba su kai su tsufa ba saboda dalilan da ke a zahiri.”

- Muiz Banire

Osinbajo ya cancanta?

Da aka tambaye shi a game da Farfesa Yemi Osinbajo, sai ya ce shi ma shekarun na sa sun yin nisa.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnatin Buhari ta ke kokarin tsawaita wa’adinta har bayan 2023 inji PDP

“Idan ka dauki ma’aunina, shi ma (Osinbajo) ba zai cancanta ba domin ina da irin ra’ayinsu Afe Babalola ne, wanda ya tsaida shekarun takara a kan 60.”

- Muiz Banire

Ba ayi wa Ibo adalci

Banire yana goyon bayan masu cewa ya kamata idan mulki ya zagayo Kudu, a bar ‘Yan kudu maso gabas su fitar da shugaban kasa domin ba su taba mulki ba.

A cewar babban Lauyan, an dade ana nunawa Ibo wariya a tafiyar siyasar Najeriya, ba a ba su mukami. Osinbajo da Tinubu kuwa sun fito ne daga kudu maso yamma.

Zaben shugaban APC

Akwai yiwuwar tsohon Gwamnan Nasarawa kuma Sanata mai-ci, Abdullahi Adamu ya karbi shugabancin APC daga hannun Gwamna Mai Mala Buni

Alamu su na nuna Sanata Abdullahi Adamu zai karbi ragamar jam’iyyar APC mai mulki daga hannun shugaban riko ba tare da ya samu wata hamayya ba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Nan da yan sa'o'i Buhari zai rattafa hannu kan sabuwar dokar zabe, Femi Adesina

Asali: Legit.ng

Online view pixel