Yanzu-Yanzu: Malami ya janye tuhumar da ake wa tsohon gwamnan Imo kan wasu laifuka

Yanzu-Yanzu: Malami ya janye tuhumar da ake wa tsohon gwamnan Imo kan wasu laifuka

  • Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya janye tuhumar da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, na aikata laifi ta yanar gizo
  • Ana dai tuhumar Ohakin da hadiminsa, Chinedu Okpareke da barazanar yada hotunan tsaraicin wata tsohuwar hadimarsa, Chinyere Amuchinwa
  • Sai dai da aka kira shari'ar a yau Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, sai lauyan da ke wakiltan Atoni Janar, Sani Bagudu, ya nemi a janye shari’ar

Abuja - Babban Atoni Janar na tarayya, Abubakar Malami ya janye tuhumar da ake yiwa tsohon gwamnan Imo, Ikedi Ohakim, na aikata laifi ta yanar gizo a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, jaridar The Nation ta rahoto.

Laifin da ake tuhumarsa a kai

Da farko dai mun kawo cewa Ofishin sifeta janar na 'yan sanda ya gurfanar da tsohon gwamnan na Imo, a gaban kotu bisa laifin tozarta wata hadimarsa, Chinyere Amuchinwa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An bindige shugaban al'umma dake jiran gadon Sarauta a cikin gida, Allah ya masa rasuwa

Yanzu-Yanzu: Malami ya janye tuhumar da ake wa tsohon gwamnan Imo kan wasu laifuka
Malami ya janye tuhumar da ake wa tsohon gwamnan Imo kan wasu laifuka Hoto: The Nation
Asali: Facebook

An tattaro cewa an gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da wani Chinedu Okpareke gaban Taiwo Taiwo, alkalin babbar kotun tarayya, bisa laifuka 5 wadanda suke da jibi da yanar gizo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana zarginsa da tsoratar da wata Amuchuenwa da cewa zasu saki hotunan tairaicinta matsawar bata sauke karar ta da tayi akan su ba na yunkurin garkuwa da ita.

Shari'ar ta koma hannun Malami

Daga baya sai babban Atoni Janar na tarayya ya karbi shari’ar, sannan a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, lokacin da aka kira shari’ar, sai lauyan da ke wakiltan Malami, Sani Bagudu ya nemi a janye shari’ar.

Bagudu ya nemi a janye shari’ar ne domin ba ministan shari’ar daman yin nazari kan takardar shari’ar da kuma daukar matakin da ya dace, rahoton Leadership.

Bayan bukatar da Bagudu ya gabatar wanda lauyan mai shari’a, Taiwo Taiwo, bai nuna adawa da shi ba, sai aka soke tuhumar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna

Harkallar kwaya: Kotu a Abuja ta ce NDLEA ta duba bukatar belin Abba Kyari cikin awa 48

A wani labarin kuma, wata babbar kotu a Abuja, a ranar Alhamis, ta umurci hukumar NDLEA, cikin sa’o’i 48, ta amsa bukatar da DCP, Abba Kyari, wanda a halin yanzu yake hannunta, ya shigar na neman belinsa bisa rashin lafiya.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da wannan umarni ne a ranar da hukumar NDLEA ta yi ikirarin cewa ba a kai mata bukatar Kyari ba, Vanguard ta rahoto.

Lauyan hukumar Mista Mike Kasa, ya shaida wa kotun cewa har yanzu bai samu kwafin bukatar belin da ke kunshe da karar Abba Kyari mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel