An bindige Shugaban al'umma dake jiran gadon Sarauta har cikin gida, Allah ya masa rasuwa

An bindige Shugaban al'umma dake jiran gadon Sarauta har cikin gida, Allah ya masa rasuwa

  • Wasu mahara sun halaka shugaban al'umma, Honorabul Sunday Idenyi, da tsakar dare a cikin gidansa a jihar Ebonyi
  • Rahoto ya nuna cewa ƙafin rasuwarsa yana ɗaya daga cikin mutanen da ake tsammanin zasu gaji Sarautar yankinsa
  • Har zuwa yanzun hukumar yan sanda reshen jihar Ebonyi ba ta ce komai ba game da lamarin, gwamnati tace ba zata ce komai ba

Ebonyi - Wasu da ba'a san ko suwaye ba sun bindige Honorabul Sunday Idenyi, tsohon shugaban cibiyar cigaban Ngbo ta gabas a ƙaramar hukumar Ohankwu, jihar Ebonyi.

Daily Trust ta tattaro cewa an naɗa shi shugaban cibiyar ne a shekarar 2015, kuma ya jagorance ta har zuwa shekarar 2019.

Marigayi Idenyi ya rasa rayuwarsa ne ranar Litinin da daddare a mahaifarsa wato Amoffia Ngbo, jihar Ebonyi.

Yan ta'adda
An bindige Shugaban al'umma dake jiran gadon Sarauta har cikin gida, Allah ya masa rasuwa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa sau bakwai aka harbe shi yayin da maharan suka mamaye gidansa ɗauke da manyan makamai masu hatsari.

Kara karanta wannan

Mulki ba naku bane: Obasanjo ya shawarci tsoffin da ke neman tsayawa takara a 2023

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa shekarar da ta gabata marigayin ya rasa kaninsa na jini ta irin wannan hanya, aka masa kisan gilla.

Kafin rasuwarsa, Idenyi na ɗaya daga cikin sunayen yan takarar da ake tsammanin ɗayansu zai gaji Kunerar Basaraken yankin Amoffia Ngbo, kamar yadda Sunnews ta rahoto.

Wane mataki hukumomin gwamnati suka ɗauka?

Har yanzun da muke kawo muku wannan rahoton, ba'a samu wayar kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Ebonyi, DSP Loveth Odah, ba, domin jin ta bakin hukumarsu.

Amma mai bada shawara ga gwamnatin jihar kan harkokin tsaro, Mista Emeagha Okoro, ya shaida wa wakilan mu cewa hukumar yan sanda ce kaɗai ke da alhakin tsokaci kan lamarin.

Ya ce:

"Ku yi hakuri ku cigaba da lalubar kakakin yan sandan a waya, domin ita kaɗai ke da alhakin tabbatar da faruwar lamarin."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisa ta tsige mataimakin shugaba, wasu yan majalisu biyu sun yi murabus

A wani labarin kuma Wani mutumi da aka ce ya mutu ya dawo gida bayan shekara 5, Matarsa ta guje shi

Wasu iyalai yan Najeriya sun shiga rudani bayan dawowar wani ɗan su wanda aka bayyana cewa ya bace kuma ya rasa rayuwarsa.

Mutumin ya ɓata ne yayin tafiya a cikin jirgin ruwa a Kamaru, ya dawo gida bayan shekara 5 amma ya tarad da matarsa ta sake Aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel