Barazanar yada hotunan tsiraicin budurwa: Tsohon gwamna zai gurfana a gaban kotu

Barazanar yada hotunan tsiraicin budurwa: Tsohon gwamna zai gurfana a gaban kotu

- Ofishin sifeta janar na 'yan sanda zai gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo akan zargin tozarta wata budurwa

- Ana zargin tsohon gwamna Ikedi Ohakim da wani Chinedu Okpareke da yunkurin sakin hotunan tsiraicin wata Chinyere

- An kama Okpareke, amma hukuma ta bayar da belinsa bayan ya cika sharuddan beli sannan zai gurfana gaban kotu ranar 15 ga watan Fabrairu

Ofishin sifeta janar na 'yan sanda zai gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, a gaban kotu a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu bisa laifin tozarta wata Chinyere Amuchinwa.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, za a gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da wani Chinedu Okpareke gaban Taiwo Taiwo, alkalin babbar kotun tarayya, bisa laifuka 5 wadanda suke da jibi da yanar gizo.

An kama Okpareke amma an sake shi bayan ya cika sharuddan beli.

Ana zarginsa da tsoratar da wata Amuchuenwa da cewa zasu saki hotunan tairaicinta matsawar bata sauke karar ta da tayi akan su ba na yunkurin garkuwa da ita.

KU KARANTA: Fani-Kayode ya tunkare ni da batun sauya sheka zuwa APC, Yahaya Bello

Barazanar yada hotunan tsiraicin budurwa: Tsohon gwamna zai gurfana a gaban kotu
Barazanar yada hotunan tsiraicin budurwa: Tsohon gwamna zai gurfana a gaban kotu. Hoto daga dailynigerian.com
Source: UGC

Karar wacce ta kai a ranar 25 ga watan Nuwamban 2020 da lauya, M. O. Omosun ya sanya hannun cewa Ohakim da Okpareke "bisa sani kuma da ganganci sun tura wani sako ta yanar gizo na cutarwa da tozarta Amuchienwa".

Kamar yadda 'yan sanda suka tabbatar, laifi ne hakan karkashin bangare ba 24(1)(a) na laifin yanar gizo Act 2015.

Kamar yadda aka gabatar da laifukan: "Chinendu Okpareke 'm' 49, da Dr Ikedi Ohakim 'm' da wasu sun hada kai a ranar 13 ga watan Augustan 2020 bisa ganganci da mugunta suka tura hotunan tsiraici don tozarta wata Chinyere Amuchienwa 'f' ta yanar gizo, don haka sun aikata laifi karkashin bangare na 27 (1)(a) na laifin yanar gizo Act 2015.

"Cewa matsalar bada janye karar ku da tayi akan yunkurin garkuwa da ita ba, zaku saki hotunan tsiraicinta a CNN don duniya ta gani, hakan laifi ne mai girma."

KU KARANTA: Alkali ya sabunta laifukan da ake zargin dan hadimin Tambuwal da wasu mutum 2

A wani labari na daban, wgamnatin daular Larabawa (UAE) ta dakatar da shigar da 'yan Najeriya zuwa Dubai a matsayin hanyar dakatar da yaduwar cutar COVID-19.

Wannan umarnin ya biyo bayan sa'o'i 24 da da jiragen UAE suka sanar da wannan dakatarwar jirage daga Legas zuwa Abuja.

Babban kamfanin jiragen da yake kai mutane Dubai daga Najeriya, Air Peace, ya sanar da wannan umarnin na UAE ga fasinjoji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel