Bidiyon yaye dalibai: Lakcaran Abuja ya nade jamfarsa, ya tiki rawa a wurin bikin yaye dalibai

Bidiyon yaye dalibai: Lakcaran Abuja ya nade jamfarsa, ya tiki rawa a wurin bikin yaye dalibai

  • An ga wani lakcara dan Najeriya a jami'ar Abuja yana tika rawa cikin nishadi a wani faifan bidiyo mai ban dariya da ke yawo a kafafen sada zumunta
  • Bidiyon ya nuna yadda malamin na jami'a ke tika rawar ban dariya a yayin taron yaye dalibai na jami'ar
  • Bidiyon ya sa mutane da yawa nishadi kasancewar rawar tasa ba kamar yadda aka saba gani bane a irin wuraren

Wani lakcara a Jami’ar Abuja (UNIABUJA) ya tika rawa a bainar jama'a, sakamakon rawarsa ya ba da citta sosai, domin kuwa an sha dariya.

Malamin jami'ar ya tika rawa cikin nishadi a lokacin da jami'ar ke bikin yaye dalibai, wanda ya ja hankalin sauran mahalarta taron.

Lakcara ya tiki rawa a bainar jama'a
Bidiyon yaye dalibai: Lakcaran Arewa ya nade jamfarsa, ya tika da rawa a wurin biki | Hoto: @gossipmillnaija
Asali: Instagram

Rawar da ba a saba gani ba

Malamin da ke sake sanye da jamfa ya tika rawarsa shi kadai, lokaci-lokaci yakan tsaya ya yi magana da mutumin da ke kusa dashi, alamun da ke nuna yana gayyatar na kusa dashi ya zo su cashe tare.

Kara karanta wannan

Shin za ka tsaya takara a 2023: Jonathan ya ba da amsar da ba a yi tsammani ba

Rawar tasa dai ba a saba ganin irinta ba, kuma ta ba da dariya matuka. Ya juyo sau da yawa ko lokacin da yake rike da jan ambulan a hannunsa na hagu. Nan take jama'a suka yi ihun nuna nishadantuwa.

Kalli bidiyon:

'Yan soshiyal midiya sun yi martani

Yayin da bidiyon mai ban dariya ya hau kafar Instagram, @gossipmillnaija ya yada shi, ya jawo cece-kuce daga mutane da dama.

Ga kadan daga martanin jama'a:

@zayee_nab tace:

"Lokacin da dalibinku masu matsala suka kammala karatunsa kenan."

@brownsonsani yayi sharhi:

"Kullum aiki babu rawa shi yasa warisi ya zama dolo."

@imperryblink ya mayar da martani:

"Mutumin bai sauraran wakokin, yana rawa ne kawai kuma ya riga ya bayyana min abubuwa."

@rolat_abiola_olaide ya ce:

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

"Mafi yawan matsalan dalibai ne watakila za su kammala karatu."

@_moni_car:

"Kar ku ga laifinsa, watakila yaronsa na cikin daliban."

@charming._caramel ne ya rubuta

"Lakracocri ma ai mutane ne... sun cancanci jin dadi, na rantse."

Wata Sabuwa: Ango ya halarci wurin ɗaura aurensa da tsofaffin kananan kaya, Mutane sun masa rubdugu

A wani labarin, ma'aurata kan yi iyakacin bakin kokarin su wajen tabbatar da sun fita fes-fes ranar daura auren su ko da kuwa haya ne su kan dakko na kaya dan kyautata wannan ranar.

Sai dai a wani biki kam ba'a ga irin haka ba tare da wani mutumi da ya Angonce da Amaryarsa.

Angon ya fito cikin wata bakar riga da kuma wandon Jeans da aka wanke kuma ya fara kodewa, ko kadan kuma babu wata alamar damuwa a fuskarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel