Kano: 'Yan Sanda Sun Kwace Tabar Wiwi Da Tramadol Na Naira Miliyan 52

Kano: 'Yan Sanda Sun Kwace Tabar Wiwi Da Tramadol Na Naira Miliyan 52

  • Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kwace kwalayen tramadol 1,042 da dauri-daurin tabar wiwi guda 559, masu kimar N52,015,000 yayin da ake kokarin shigar dasu jihar cikin shekara daya
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Sumaila Shuaibu Dikko ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai jiya dangane da matsalolin shaye-shaye a jihar
  • A cewarsa, sun kwace katan-katan na magunguna marasa kyau masu kimar N2,400,000, da kuma kwalayen extol da kwalaben sauran kayan maye na miliyoyin nairori

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta samu nasarar kwace kwalayen tramadol, dauri-dauri na tabar wiwi da sauran kayan maye cikin shekara daya a jihar, The Sun ruwaito.

Sumaila Shuaibu Dikko, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tabbatar wa da manema labarai hakan a jiya inda ya koka akan yadda jama’a suke amfani da kayan maye sosai a jihar.

Kara karanta wannan

Wawure kudin kasa: Kotu ta tasa keyar tsohuwar minista da wasu mutane 2 zuwa gidan yari

Kano: 'Yan Sanda Sun Kwace Tabar Wiwi Da Tramadol Na Naira Miliyan 52
'Yan Sanda A Kano Sun Kwace Tabar Wiwi Da Tramadol Na Naira Miliyan 52. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

A cewarsa, sun kwace kwalaye da dama na lalatattun magunguna masu kimar N2,400,0000, kwalayen extol masu kimar N51,045,000; kwalaben codeine guda 150, kwalayen kwayar diazepam guda 3,085 da kwalayen diclofenac duk a cikin shekara guda daya.

Kamar yadda ya shaida, sun kama mutane 2,606 wadanda suka aikata laifuka daban-daban a jihar inda ya ce yanzu haka an kama wasu da ake zargin ‘yan fashi ne guda 264, masu yi wa mata fyade 88, wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, wasu mutane 140 da ake zargin suna garkuwa da jama’a da sauran mutane 34 da ake zargin su da aikata kisan kai.

Ya lissafo nasarorin da suka samu ciki har da ceto mutane daga masu garkuwa da jama’a

Ya ce wadanda aka kama cikin lokacin sun hada da mutane 12 da ake zargin su da safarar jama’a, mutane 89 ‘yan damfara, mutum 179 da ake zargin suna safarar miyagun kwayoyi, 12 masu harkar gidajen gyaran halin bogi da wasu mutane 33 da ake zargin suna satar shanu, rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Dagaci Da Matansa 2 Tsawon Mako 3 a Neja Sun Nemi a Biya Kuɗi a Fanshe Su

Yayin lissafo nasarorin da suka samu cikin shekara daya a jihar, ya ce sun samu nasarar ceto mutane 160 da aka daure ba tare da sun aikata komai ba, 40 bayan masu garkuwa da mutane sun sace su sai kuma wasu mutane 9 da masu safarar mutane suka sace.

Katsina: 'Yan sanda sun kama wani da ke yaudarar mata ya kwana da su a otel ya kuma sace musu waya da kuɗi

A wani labarin, jami'an yan sanda a Jihar Katsina sun kama wani mutum mai shekaru 31 da ake zargin yana amfani da intanet wurin yaudarar mata yana kwanciya da su a Kano, Vanguard ta ruwaito.

An shaida wa manema labarai cewa wanda ake zargin, Usama Tijjani, mazaunin Daurayi Quaters ne a karamar hukumar Gwale a Jihar Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel