Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Dagaci Da Matansa 2 Tsawon Mako 3 a Neja Sun Nemi a Biya Kuɗi a Fanshe Su

Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Dagaci Da Matansa 2 Tsawon Mako 3 a Neja Sun Nemi a Biya Kuɗi a Fanshe Su

  • Bayan kwashe makwanni uku a hannun ‘yan bindiga, sun bukaci kudin fansar dagacin kauyen Beni na karamar hukumar Munya da ke Neja, Alhaji Jafaru Umar Sarki Naira miliyan 5
  • ‘Yan bindigan wurin 60 sun kai farmaki kauyen ne a ranar 2 ga watan Fabrairu inda suka sace dagacin, matan sa guda biyu da sauran jama’an gari 15
  • A harin, sun halaka kusan mutane 5 wanda sanadin hakan jama’a suka tsere garin Kafin-Koro da ke karamar hukumar Paikoro don neman tsira

Neja - Bayan dagacin kauyen Beni, Alhaji Jafaru Umar da ke karamar hukumar Munya ya kwashe fiye da makwanni uku a hannun ‘yan bindiga sun bukaci Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa, The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An kama wata mata mai shekaru 30 da ta ƙware wurin siyayya da jabun N1,000 a kasuwa

A farmakin da suka kai kauyen ranar 2 ga watan Fabrairu, kusan makwanni uku da suka gabata, sun sace dagacin, matan sa guda biyu da kuma fiye da mutane 15.

Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Dagaci Da Matansa Tsawon Mako 3 a Neja Sun Nemi a Biya Kuɗi a Fanshe Su
Yan bindiga da suka sace dagaci da matansa a Neja sun nemi kudin fansa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakamakon farmakin, sun halaka kusan mutane biyar wanda hakan ya tarwatsa kauyen, jama’a suka dinga guduwa Kafin-Koro da ke karamar hukumar Paikoro.

Kamar yadda wata mata wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida, ‘yan bindigan yanzu haka suna bukatar N500,000 don sakin ko wanne cikin mutane 15 din da suka sace.

Ta wayar dagacin kauyen suka tuntubi jama’a

A cewarta:

“A ranar Laraba da dare sun yi amfani da lambar dagacin kauyen don tattaunawa da mu. Da farko sun bukaci naira miliyan 5 don fansar dagacin kauyen.
“Amma bayan rokon su tare da sanar da su cewa mutumin ya biya kudaden fansa da dama a shekaru biyu da suka gabata na yaransa da jama’an gari, sai suka yarda mu bayar da naira miliyan 2.5. Amma sun ce ko wanne mutum cikin wadanda suka sace sai an biya mishi N500,000 na fansa.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Bindige Mutum Ɗaya, Sun Sace Wasu 10 a Tashar Jirgin Ƙasa a Kogi

“Akwai akalla mutane 15 a hannun su, ciki har da mata da yara. Gabadaya garin ya zama abin tsoro tun bayan harin da suka kai farkon watannnan.”

‘Yan bindiga sun tasa kauyen Beni gaba

Kauyen Beni da ke karamar hukumar Munya kamar yadda The Sun ta ruwaito ya yi fice a noma cikin jihar, kuma ‘yan bindiga sun dade suna kai wa kauyen farmaki. Ba sa samun wani dauki ko tallafi ta ko ina.

Tsakanin 2020 da 2021, ‘yan bindiga sun kai hare-hare kusan sau 11, inda suka halaka fiye da mutane 26 sannan suka yi garkuwa da fiye da mutane 70 tare da amsar kudin fansa kusan naira miliyan 20 daga ‘yan uwan wadanda suka sace.

Daya daga cikin manyan farmakin da suka kai garin shi ne na ranar 8 ga watan Janairun 2020, wanda suka halaka limamin babban masallacin Beni tare da wasu mutane 6 sannan suka yi garkuwa da mutane 49 ciki har da yaran dagacin kauyen ana saura mako daya auren su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m

Duk da dai sun bukaci Naira miliyan 49 a matsayin kudin fansa, jama’a sun dinga rokon su har suka amince da naira miliyan 9.

Sai dai duk kokarin da aka dinga yi na jin ta bakin shugaban karamar hukumar, Mallam Garba Mohammed Dazza da dan majalisar jihar yankin, Andrew Doma, abin ya ci tura don duk basu daga waya ba lokacin da aka kira su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel