Mahaifiyata da mijina sun yi shekaru 15 suna lalata: Mata ta fashe da kuka yayin bada labari a bidiyo

Mahaifiyata da mijina sun yi shekaru 15 suna lalata: Mata ta fashe da kuka yayin bada labari a bidiyo

  • Soipan Martha ta fada cikin matsananciyar damuwa bayan ta gano yadda mahaifiyarta da mijin ta ke cin amanar ta na tsawon shekaru 15
  • An ji yadda mahaifiyarta ta kira ta da tsakar dare, inda take rokon ta da ta ceci rayuwarta daga mijin ta wanda yanzu suka rabu
  • Mahaifiyarta tayi alkawarin kawo karshen kazamar mu'amalar, sai dai, kwanan nan ta gano yadda biyun suka sake komawa juna

A lokacin da Soipan Martha take girma, ta yi burin samun soyyayar mahaifiyar ta, sai dai bata taba fahimtar dalilin da yasa hakan bai samu ba.

Lokacin tana 'yar shekara biyu, mahaifiyarta ta barta karkashin kulawar yayar ta, sannan ta tafi Saudi Arebiya don neman arzikin duniya. Ta bayyana yadda rayuwa bata mata dadi ba, yayin da take tunanin lokacin da za ta kara ganin mahaifiyar ta.

Kara karanta wannan

Budurwa na bukatar kudin raino daga mawaki Tekno bayan ta kunshi ciki yayin sauraron wakarsa

Mahaifiyata da mijina sun yi shekaru 15 suna lalata: Mata ta fashe da kuka yayin bada labari a bidiyo
Mahaifiyata da mijina sun yi shekaru 15 suna lalata: Mata ta fashe da kuka yayin bada labari a bidiyo
Asali: Original

Wata rana, mahaifiyarta ta dawo daga Kenya, inda ta yanke shawarar kai ta makarantar kwana, amma babu mai kai mata ziyara a ranar da ake kai ziyara. Hakan yasa ta samu kusanci da shugabar makarantar, wacce ta sha alwashin rike ta kamar ita ta haife ta kuma tayi hakan.

Da taimakon kakarta, ta shiga makarantar sakandari bayan kammala firamaren, da haka ne ta fara aiki a sashin karamci, inda ta hadu da wani mutum, har suka fara soyayya. A rashin sa'a, ta fada soyyaya da mutumin banza.

"Na yi zaton yana kauna ta, saboda irin kulawar da yake bani. Amma bayan na koma gidanshi, daga nan ne matsalar ta fara.
"A rana ta farko da nayi a gidanshi, ya nadamin duka, sannan ya bukaci in bashi kudi da katikan cire kudi na asusun banki na. A duk lokacin da na rasa kudi, ya na siyar da waya ta ya adana kudin," ta bayyana wa wani dan jarida da ta yarda dashi.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina

Martha ta ce, a duk sanda ta bukaci taimako daga mahaifiyar ta, uwar tana kare mutumin, ta hanyar cewa ba zai taba aikata hakan ba.

Martha ta tuna yadda wata rana dan uwan mijinta ya gabatar da ita a gun mahaifiyar mijinta, yadda ta amsa mata ya matukar bata mamaki.

"Ta tambayeni duk da irin wannan kyawun, meyasa baki samu wani kin aura ba?" Martha ta bada labari, inda ta kara da, sai yar uwar mijin ta bayyana mata yadda mutane da dama suka neme ta, amma wasu daga cikin su sun koma a nakasassu, wasu kuma da raunuka masu tsanani.

A ranar da ta dawo daga gabatarwan, ta tarar da mijin ta cikin fushi. Ya so jin abunda 'yan uwanshi suka fada mata. Bayan ta ki bashi amsa, ya nada mata bakin duka, sai da ta fita hayyacin ta.

Kawai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti, inda ake shaida mata cewa tana da ciki, amma ta rasa jinjirin bayan awa uku da haihuwa.

Kara karanta wannan

Ta Musamman ce: Bidiyon yadda mata ta biya wa mijinta bashin N1.3m ya bar jama'a baki bude

Martha ta nemi kariya a Majami'a, inda wani fasto yayi amfani da damar ya dirka mata ciki. Sannan ya guje ta bayan ta shaida mishi game da cikin. Amma a rashin sa'a, bayan wata tara, ta matukar shan wahala a nakudar da ta zama barazana ga rayurwata da na jinjirin, sannan ta haifi namiji.

A wannan matakin, Martha ta yanke shawarar sabunta rayuwa ita da yaron ta kadai, sai dai bada jimawa ba aka dakile kwanciyar hankalin nata;

Mahaifiyarta ta kirata tsakiyar dare, yayin da take rokon taimakon ta.

Ga mamakin abunda ta gano, "Ta bayyana min (sunan tsohon mijina) yana jibgar ta, in taimaka mata.
"Shekaru goma kafin aukuwar hakan, na rabu da mutumin nan, amma ya bayyanamin yadda ya dauka tsawon shekaru 15 yana mu'amala da mahaifiyata.
"Mahaifiyar tawa na wurin, amma ta kasa musantawa. Hakan ya bata min rai matuka. Saboda me za tayi min haka? Saboda me za ta cutar dani haka," ta koka cikin matsananciyar damuwa.

Kara karanta wannan

Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

Babu dadewa mahaifiyar ta fara ciwo, hakan yasa ta koma wurin Martha, saboda mutumin ba zai iya kula da ita ba.

Karyar da ta sharara mata

"Har tana min karyar sun kawo karshen ma'amalar banzar da suke yi, amma bayan na kula da ita, har ina ciyo bashi saboda kula da lafiyar ta, maihaifiyar tawa ta kwashe komatsanta ta bar gida na zuwa gidan tsohon mijina,'" Martha ta tuna.

Inda ta kara da cewa, ta dade da nisanta kanta daga biyun, amma ta yafe musu. Ta na fatan sake sabuwar rayuwa, sannan ta na da burin ganin ta biya basukan da ake bin ta, sannan ta bar kasar zuwa wurin da babu wanda ya san damuwar da ta shiga a baya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel