Budurwa na bukatar kudin raino daga mawaki Tekno bayan ta kunshi ciki yayin sauraron wakarsa

Budurwa na bukatar kudin raino daga mawaki Tekno bayan ta kunshi ciki yayin sauraron wakarsa

  • Wata budurwar 'yar kasar Zambia ta bukaci mawakin Najeriya Tekno da ya biya ta kudin raino sakamakon cikin da ta kunsa yayin da take jin wakarsa
  • A cewar budurwa wacce yanzu tace ta gaji da rainon dansa kuma ta na bukatar kudi daga wurinsa, dadin wakarsa mai suna Pana tasa ta kwanta da namiji
  • Rita Mwayanda ta kara da sanar da cewa, bata san lokacin da ta samu cikin ba saboda tsabar zumudi da dadin wannan waka tashi

Wata mata 'yar kasar Zambia mai suna Rita Mwayanda ta yi kira ga mawakin Najerya Tekno, wanda ta yi ikirarin cewa wakarsa ta kunsa mata ciki.

Mwayanda ta yi ikirarin cewa Tekno ya saki wakarsa mai suna ‘Pana', dadi ya kama ta kuma ta kwanta da namiji, wanda hakan ne yayi sanadiyyar samun cikinta. Ta cigaba da neman kudin raino daga mawakin Najeriyan.

Kara karanta wannan

An kama wata mabaraciya da kudi har N500,000 da dala 100 a Abuja, an tsare ta

Budurwa na bukatar kudin raino daga mawaki Tekno bayan ta kunshi ciki yayin sauraron wakarsa
Budurwa na bukatar kudin raino daga mawaki Tekno bayan ta kunshi ciki yayin sauraron wakarsa. Hoto daga DJ-C Money Worldwide
Asali: Facebook

Rahoton da wani mai nishadantarwa na kasar Zambia mai suna DJ C-Money ya rubuta a shafinsa na Facebook, ya ce:

"Ya dace akwai bukatar Tekno ya biya kudin rainon jaririnsa. Ba zan iya cigaba da wahalar masa ba," 'Yar kasar Zambia ta koka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata budurwa 'yar kasar Zambia mai suna Rita Mwayanda ta bayyana tana bukatar mawakin Najeriya Tekno ya biya ta kudin raino saboda dalilinsa ta samu ciki kuma take fama.

Ta yi bayanin cewa:

"Can a shekarar 2016. Ina matukar kaunar wakar Tekno. Har zuwa kowacce mashaya nake yi domin sauraron wakar Tekno. A watan da ya saki wakarsa mai suna ‘Pana’ na cika da zumudi har na kwanta da namiji ban sani ba wanda hakan yasa na samu juna biyu.
"Ba don saboda Tekno ba, da yanzu bani da dan da zan nemi kudin raino daga wurinsa."

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina

Matashi mai shekaru 19 ya dirka wa malamar shi mai shekaru 28 ciki, za ta haife shi

A wani labari na daban, Richard Nana Sam, dan kasar Ghana ne wanda ransa yayi matukar baci, sanadiyyar wani lamari dake wakana a gidan shi, wanda ya yanke shawarar fallasa wa a kafafan sada zumuntar zamani, da sa ran samun mafita.

Yayin bada labarin kalubalen da yake fuskanta a wata sananniyar kungiyar 'yan Ghana dake da shafi a Facebook, ya kwashe labarin tun daga farko har karshe.

Richard ya bayyana yadda yayi wa yaran shi tagwaye (namiji da mace) masu shekaru 19 hayar malamar da za ta dunga koya musu karatu a gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel