Ni 'yar Dirama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

Ni 'yar Dirama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth

  • Fitacciyar jaruma Maryam Booth, ta fusata inda ta yi wata wallafa cike da fushi da zafin rai bayan wasu sun tabota kan batun sarkin waka
  • Maryam Booth ta ce ita 'yar fim ce, 'yar drama kuma'yar nanaye kamar yadda ake fadi, babu shakka ta na alfahari da zama hakan
  • Ta bukaci jama'a da su fita daga harkarta sannan su daina kutse cikin rayuwar ta tunda babu wanda ya isa yayi mata hukunci

Sannanen abu ne cewa a makon da ya gabata masana'antar Kannywood ta rincabe tare da rikicewa da hargitsi tun bayan batun Ladin Cima da kuma bidiyon Naziru Sarkin waka inda ya zargi cewa ana lalata da 'yan matan masana'antar kafin a saka su a fim.

A daren jiyar Lahadi ne jaruma Nafisa Abdullahi ta saki takarda inda ta yi wa Sarkin wakan martani kan ikirarinsa.

Babu dadewa kuwa jaruma Maryam Booth ta sake wallafa takardar a shafin ta tare da bayyana cewa abokiyar aikin ta ta gama fadin komai da ta yi niyyar fadi.

Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth
Ni 'yar Drama ce, 'yar Nanaye, ina alfahari da hakan, Maryam Booth. Hoto daga @officialmaryambooth
Asali: Instagram
"Ba na tunanin akwai wani abu da ya rage da zan ce saboda kin sace kalamai na," ta wallafa da harshen turanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu bata lokaci jama'a suka fara yi wa Booth martani inda suke cewa ashe ta na da bakin magana? Ita me ya rage ba a gani ba?

Wannan al'amarin ya tunzura jarumar inda a take ta je ta sake yin wata wallafa wacce Legit.ng ta gani. Sai dai bayan kankanin lokaci jarumar ta cire wallafar amma mun sake samowa daga shafin Kannywood empire.

A cikin wallafar da ta yi cike da zafin rai, ta sanar da cewa ita 'yar drama ce kuma 'yar nanaye kamar yadda ake fadi, ta na alfahari da hakan kuma babu wanda ya isa ya mata hukunci.

Wallafar ta ce:

"Ni 'yar fim ce, 'yar drama, 'yar nanaye kamar yadda ku ke kiranmu kuma ina alfahari da hakan. Ina alfahari da duk wanda ke masana'antar. Abu daya da nake son ku gane kenan.
"Abu na biyu kuwa, idan har mutum zai yi zargi kan wani abu to ya dinga bada misali a ce misalin wane da wane domin karin bayani.
"Hakazalika, idan har wani ko wata yana so ya kawo rayuwata a matsayin misalin abubuwan da ke faruwa, tambayata a nan shi ne, kai wa ye da za ka yanke min hukunci? Rayuwata dai tawa ce kuma nima bani da wani iko a kan taka amma idan kana son dora matsalata a kan ka, toh ka zuba ido ka cigaba."

Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka

A wani labari na daban, kamar yadda Legit.ng ta gano, batun da yafi yi wa 'yan Kannywood zafi a maganar sarkin waka shi ne batun lalata da mata kafin a saka su a fim inda matan Kannywood ke ta fitowa suna musanta waccan maganar da yayi.

Jaruma Nafisa Abdullahi ta rubuta budaddiyar wasika cikin harshen turanci a shafinta na Instagram kuma ta kara da bayani a kasan wasikar da harshen Hausa inda ta bayyana cewa babban zargi ya fitar tunda ta na cikin matan masana'antar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel