Yanzu-Yanzu: ASUU ta shiga ganawar sirri da gwamnatin tarayya a Abuja

Yanzu-Yanzu: ASUU ta shiga ganawar sirri da gwamnatin tarayya a Abuja

  • Gwamnatin tarayyan Najeriya ta fara tattaunawa domin shawo kai da kuma kawo karshen yajin aikin ASUU a Abuja
  • Ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Dakta Ngige, ya ce za'a maida hankali wurin nemo bakin zaren a taron su na yau Talata
  • Taron ya kunshi wakilan ASUU, da wakilan gwamnatin tarayya na ma'aikatu da dama da suke da rawar takawa wajen kawo karshen lamarin

Abuja - Gwamnatin tarayya ta fara ganawa da wakilan kungiyar Malaman jami'o'i ASUU, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Taron wanda ke wakana a ɗakin taro na ma'aikatar kwadugo da samar da ayyukan yi, ya samu halartar kusoshin gwamnatin tarayya daga ma'aikatu daban-daban.

Shugaban ASUU da Ministan Kwadugo
Yanzu-Yanzu: ASUU ta shiga ganawar sirri da gwamnatin tarayya a Abuja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Daga cikin waɗan da suka halarci taron har da wakilan ma'aikatar ilimi, ma'aikatar kuɗi da tsare-tsaren ƙasa, ofishin shugaban ma'aikata, hukumar NUC, da Ofishin Akanta Janar na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An bindige shugaban al'umma dake jiran gadon Sarauta a cikin gida, Allah ya masa rasuwa

Wane abu za'a tattauna a wurin taron?

Ministan Kwadugo da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, yace taron zai maida hankali ne kan tattaunawar neman matsaya tsakanin ASUU da FG.

A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, kungiyar ASUU ta sanar da shiga yakin aiki a faɗin jami'o'in gwamnatin Najeriya kamar yadda Channels tv ta rahoto.

A cewar kungiyar ta cimma matsayar shiga yajin aikin gargaɗi na tsawon makonni hudu bisa gazawar gwamnatin tarayya na cika mata alƙawurranta.

Wannan dai na zuwa ne bayan kungiyar ɗalibai ta ƙasa NANS ta yi barazanar fara zanga-zanga faɗin Najeriya matukar ba'a janye yajin aiki ba.

A wani labarin kuma Gwamnan jam'iyyar PDP ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnati daga aiki

Gwamnan jahar Akwa Ibom ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnatinsa daga bakin aiki ranar Talata.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnati daga aiki

Rahoto ya nuna cewa sabanin siyasa ne ya shiga tsakanin kusoshin jihar kuma ya yi awon gaba da kujarar ta Chief Of Staff.

Asali: Legit.ng

Online view pixel