Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnati daga aiki

Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnati daga aiki

  • Gwamnan jahar Akwa Ibom ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnatinsa daga bakin aiki ranar Talata
  • Rahoto ya nuna cewa sabanin siyasa ne ya shiga tsakanin kusoshin jihar kuma ya yi awon gaba da kujarar ta Chief Of Staff
  • Tuni a aka umarci tsohon shugaban ma'aikatan ya mika dukkan kayayyakin gwamnati dake hannunsa ga sakataren gwamnati

Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnatinsa, Ephraim Inyangeyen, daga bakin aiki yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a jihar.

Premium Times ta rahoto cewa sanarwan sallamar ta fito ne ranar Talata, a wata takarda da Sakataren gwamnati, Emmanuel Ekuwem, ya aike wa Chief of Staff.

Rahotanni sun bayyana cewa sabanin siyasa ya shiga tsakanin Mista Inyangeyen da Gwamna Emmanuel, wanda abokanan juna ne sosai.

Kara karanta wannan

Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023

Gwamna Udom Emmanuel
Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnati daga aiki Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Tsohon shugaban ma'aijatan ya fara rike mukamin kwamishinan ayyuka da gidaje kafin daga bisani gwamnan ya maida shi mukamin Chief Of Staff.

Gwamnan ya bayyana cewa sallamar babban kusan gwamnatin na da alaƙa da sanin makamar aiki da kuma, "Gogewar aiki."

Daily Trust ta rahoto Wani sashin wasikar sallamar ya ce:

"Bisa bukatar gaggawa ta samun mai kwarewa da gogewar da zai iya tafiyar da haɓaka tattalin arziki cikin sauƙi, ba'a bukatar aikin ka a wnanna matsayi kuma an kore ka daga muƙamin shugaban ma'aikata."
"Sabida haka ana umartarka da ka miƙa dukkan kayayyakin gwamnati dake hannunka ga Sakataren gwamnatin jiha."

Meya haɗa manyan mutanen biyu?

A kwanan nan, Mista Inyangeyen, ya tabbatar da kudurinsa na neman kujerar Sanata mai wakiltar mazaɓar Akwa Ibom ta kudu, wanda ya yi hannun riga da matakin gwamna na kai kujerar wani yanki daban.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda jami'in dan sanda ya mutu a cikin gidan wani tsohon gwamna

Bayan haka, Tsohon shugaban ma'aikatan na goyon bayan Sanata Bassey Albert, ya gaji Kujerar gwamna a 2023, wanda ya saba wa ra'ayin gwamna Emmanuel dake bayan Eno Umo.

A ranar Lahadi aka zare jami'an tsaron dake tare da shi, bayan ya ce ba shi mutane zasu tuhuma ba idan ba'a kammala ayyukan da gwamnati ta ɗakko ba.

A wani labarin kuma Majalisar Dokoki ta tsige mataimakin kakaki, yan majalisu biyu sun sauya sheka zuwa APC

Majalisar dokokin jihar Ebonyi ta bayyana murabus ɗin mataimakin kakaki da wasu mambobinta biyu a zaman Litinin.

Sai dai lamarin ya tada hatsaniya, yayin da mutanen uku baki ɗaya suka musanta ikirarin majalisa, suna nan daram a matsayin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel