Gwamnatin Bauchi ta fara koyawa tubabbun karuwai 575 sana'o'i daban-daban

Gwamnatin Bauchi ta fara koyawa tubabbun karuwai 575 sana'o'i daban-daban

  • Don sauya musu tunani da karfafa su, hukumar Hisbah ta fara horar tubabbun yan gidan magajiya a Bauchi
  • Karuwan sun fito ne daga jihohin Najeriya daban-daban amma suna harkar karuwanci a jihar Bauchi
  • Gwamnati ta yi alkawarin basu jari da kyayyaki bayan kammala horon na watanni uku

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da shirin koyawa karuwai 575 dake harka a jihar ayyukan hannu don dauke hankalinsu daga harkar karuwanci da karfafasu.

Hukumar Hisbah wacce ke gudanar da shirin za ta horar da su kan aikin tela, gyaran gashi, girke-girke, gyara fuska, kiwon kaji, kiwon kifaye, aikin komfuta, dss.

Kwamishanan din-din-din na hukumar Hisbah da lamuran Shari'a, Barista Aminu Isa, a jawabin da ya gabatar da taro yace za'a kwashe watanni uku ana wannan horaswa.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Gwamnatin Bauchi
Gwamnatin Bauchi ta fara koyawa tubabbun karuwai 575 sana'o'i daban-daban
Asali: Twitter

Yace za'a horas da mutum 100 kan aikin tela da gyaran gashi, yayinda mutum 75 zasu koyi aikin gyaran girke-girke da gyaran fuska.

Hakazalika za'a horas da mutum 60 kan kiwon kaji da kifi, mutum 50 aikin komfuta, sauran 40 kuma kasuwanci.

Yace:

"Bari na jaddada cewa duk wanda bai yi kokari ba lokacin horon ba zai samu kudi da kayan jari ba. Za'a yi muku jarabawa bayan horaswa."
"Muna da jerin sunayenku da jihohinku kuma za muyi daidaito tsakaninku."
"48 daga cikin sun zo daga Abia, Enugu, da Delta; 49 daga Gombe, 56 daga Borno, Kano da Kaduna; 26 daga Jigawa, 41 daga Plateau da Adamawa; 36 daga Taraba; 25 daga Imo; 85 daga Benue, Cross Rivers, Ebonyi, Akwa Ibom; kuma 212 daga Bauchi."

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun hallaka 8, sun sace da dama a Neja

Gwamnati ta aurar da tubabbun yan gidan magajiya a Bauchi

Hukumar Hisbah ta jihar Bauchi ta aurar da wasu tubabbun yan gidan magajiya guda biyu a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an daura auren ne a daya daga cikin gidajen magajiya da ke Bayangari a cikin garin Bauchi.

Daurin auren ya samu halartan mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Danlami Kawule; kwamishinan harkokin addini, Umar Kesa; manyan jami’an gwamnati, manyan jami’an hukumar shari’a da kuma daruruwan yan gidan magajiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel