Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun hallaka 8, sun sace da dama a Neja

Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun hallaka 8, sun sace da dama a Neja

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun farmaki al'ummomi uku na jihar Neja, sun hallaka mutane da dama a yankunan
  • Hakazalika, sun sace wasu mutane da yawa, inda suka barnata dukiyoyi kamar yadda rahoto ya tattaro
  • Sakataren 'yan banga a yankunan da lamarin ya faru ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya fi karfin 'yan banga

Jihar Neja - Jaridar Daily Trust ta tahoto cewa, akalla mutane takwas ne aka kashe, yayin da aka sace 14 da suka hada da mata biyar a kauyukan Gpekure, Makuba da Galapai a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Rahoto ya tattaro cewa, al’ummomin sun kasance cikin farmakin ‘yan ta’adda tun daren Juma’a da suka fara kai hari a Gpekure, inda suka kashe mutane bakwai tare da sace wasu bakwai.

Kara karanta wannan

Neja: An sha yar dirama yayin da kansila ya fatattaki jami’an gwamnati da karnuka da yan daba

Jihar Neja: 'Yan bindiga sun kai farmaki, sun hallaka tare da sace jama'a
Sabon hari: 'Yan bindiga sun farmaki al'umma, sun hallaka 8, sun sace da dama a Neja | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Hare-haren sun tilastawa mazauna yankin da dama musamman mata da yara yin gudun hijira zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Zumba da Gwada da kuma makarantar Sakandare ta Gwamnati (GDSS) da ke Shiroro.

Wani mazaunin garin ya shaida cewa, an kai hari a Gpekure da Makuba da misalin karfe 11 na daren ranar Asabar, yayin da na Galapai aka kai harin da misalin karfe 1:00 na ranar Lahadi.

Ya ce:

“Wadannan al’ummomin suna da nisa da juna na ‘yan mitoci kadan. Garin Galapai na da ratan mitoci kadan daga Galadima-Kogo da aka kai wa hari makonni biyu da suka gabata. Ko ihu kayi daga Galadima-Kogo, wanda yake Galapai zai ji ka.”

Sakataren hukumar ‘yan banga na jihar Neja na karamar hukumar Shiroro, Ayuba Dakko, ya tabbatar da faruwar lamarin ga majiya.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

Sakataren 'yan banga Dakko ya ce:

“A Gpekure, sun kona gidaje da kayan abinci, sun kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da mata biyar da maza biyu.
"Bayan haka ne suka mamaye garin Makuba inda suka kashe mutum daya a ranar Asabar. A yau (Lahadi) da misalin karfe 1 na rana, sun kai hari Galapai inda suka yi garkuwa da mutane bakwai.
"Babu wanda ya rage a cikin waɗannan al'ummomin yanzu. Mutane sun yi gudun hijira zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Zumba, Gwada da GDSS, Shiroro.
"Na kwana a daji jiya. Mu ‘yan banga ba za mu iya tunkarar su ba saboda ba mu da irin makaman da suke da su.”

Neja: An sha yar dirama yayin da kansila ya fatattaki jami’an gwamnati da karnuka da yan daba

Kansila mai wakiltan unguwar Tudun Wada a karamar hukumar Chanchaga, Ibrahim Mai Farare, ya fatattaki jami’an Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Neja (NSEPA) da karnuka da yan daba kan gayyatarsa da aka yi ya zo ya amsa wasu tambayoyi.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Hukumar NSEPA dai na son ya amsa mata tambayoyi ne a kan wani wajen siyar da gas da yake kafawa a cikin unguwar.

Kansilan na fafatawa da yan unguwarsa ne a kan kafa wajen siyar da gas din.

Mazauna unguwar sun yi kira ga gwamnati da hukumomin da abun ya shafa a kan su dakatar da shirin kafa wajen siyar da gas din, inda suka ce hakan hatsari ne a cikinsu.

Sun yi korafin cewa ana iya samun fashawar gas din duba ga cewar akwai harkokin kasuwanci da dama a yankin da ke bukatar wuta.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa a yayin da ta ziyarci yankin, ta gano cewa akwai masu suyan kosai, giajen gasa biredi da masu siyar tsire da dama a kewaye.

Sojojin Najeriya sun kashe Buba Danfulani da kwamandojin ISWAP 4 a Sambisa

A wani labarin, ruwan bama-bamai da jirgin yakin sojin Najeriya ta yi ya halaka Amir Buba Danfulani da wasu tsagerun kwamandojin ISWAP hudu a yankunan Tumbuns da Sambisa a arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

PRNigeria ta tattaro cewa Amir Buba Danfulani ya kasance babban kwamandan ISWAP wanda ke aikin koyawa Fulani da makiyaya shiga kungiyar ta’addanci.

Ya kuma jagoranci ayyukan ‘yan ta’adda kama daga diban ‘yan leken asiri da kuma masu karbar haraji. Rundunar sojojin Najeriya karkashin Operation HADIN KAI ce ta aiwatar da hare-haren a wurare daban-daban a cikin makon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel