Da dumi-dumi: Harin jirgin yakin Najeriya ya kashe yara bakwai a Jamhuriyar Nijar

Da dumi-dumi: Harin jirgin yakin Najeriya ya kashe yara bakwai a Jamhuriyar Nijar

  • Jirgin yakin Najeriya ya yi luguden wuta kan wasu kananan yara bisa kuskure a jamhuriyar Nijar
  • Harin wanda aka yi nufin kaiwa yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar yara bakwai tare da jikkata wasu biyar
  • Gwamnan yankin Maradi, Chaibou Aboubacar, ne ya tabbatar da harin a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu

Wani hari ta sama da rundunar sojin Najeriya ta kai kan yan bindiga ya kashe kananan yara bakwai sannan ya jikkata wasu biyar bisa kuskure a kasar Nijar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wani gwamnan kasar ne ya sanar da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP hakan a ranar Lahadi, 20 ga watan Fabrairu.

Da dumi-dumi: Harin jirgin yakin Najeriya ya kashe yara bakwai a Jamhuriyar Nijar
Da dumi-dumi: Harin jirgin yakin Najeriya ya kashe yara bakwai a Jamhuriyar Nijar Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Gwamnan yankin Maradi, Chaibou Aboubacar ya ce:

“An samu kuskure a harin da jirgin yakin Najeriya ya kai kan iyakar wanda ya sauka a yankinmu a kauyen Nachade a ranar Juma’a.”

Kara karanta wannan

Shugaban kasa yana tsaka-mai-wuya ana saura kwana 8 zaben shugabannin APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wadanda abun ya cika da su sune kananan yara 12, bakwai daga cikinsu sun mutu sannan biyar sun jikkata.”

A cewar gwamnan, iyayen yaran na halartan wani taro ne sannan yaran kuma suna cikin wasa lokacin da harin ya riske su, rahoton Nigerian Tribune.

Aboubacar ya ce ya ziyarci kabarurrukan yaran a ranar Asabar da kuma wajen da aka kai harin bam din.

Jirgin yakin NAF ya yi ruwan bama-bamai kan maboyar gawurtaccen ɗan bindiga, Ali Kwaja, a hanyar Kaduna-Abuja

A wani labarin, mun kawo a baya cewa bayan samun tabbaci daga bayanan sirri, jirgin yaƙin sojin sama (NAF) ya saki ruwan bama-bamai kan sansanin yan bindiga a yankin Rijana, dake kan hanyar Kaduna-Abuja.

Daily Nigerian tace harin sojojin sama ya yi raga-raga da wurin aje makamai da ginin gawurtaccen ɗan garkuwa, Ali Kwaja, kuma ya hallaka dandazon yan bindiga.

Kara karanta wannan

Wani Mahaifi ya shararawa ɗiyar cikinsa mari, Allah ya mata rasuwa nan take a Jigawa

Yan bindigan na amfani da wannan wurin a matsayin maɓoyarsu, da kuma kaddamar da hari kan matafiya a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel