NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

  • Hukumar NDLEA ta kama wasu kudin jabu da suka kai $4.7 miliyan a Abuja da wani dattijo mai shekaru 52
  • A takardar da hukumar ta fitar, ta ce an taho da kudin ne daga jihar Legas amma an yi nasarar dakile shigarsu gari
  • An kama wata mai jego a Offa da ke Kwara da miyagun kwayoyi da suka hada da Tramadol, Swinol, Diazepam da allurar Pentazocine.

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama wasu kudin jabu a tsabarsu da suka kai $4.7 miliyan a Abuja.

A wata takarda da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce jami'an hukumar a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 18 ga watan Fabrairu sun tsare wasu kaya da aka aiko daga Legas zuwa Abuja a yankin Abaji da ke babban birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da kungiyar dillalan kwayoyi a Brazil, NDLEA

Kamar yadda Babafemi yace, kama kudin jabun ya yi sanadin da aka damke babban wanda ake zargi mai shekaru 52 mai suna Abdulmumini Maikasuwa.

NDLEA ta cafke matashi da $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi
NDLEA ta cafke matashi da $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi. Hoto daga @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

An yi kamen ne sakamakon bayanan sirri da hukumar yankin FCT ta samu kan bayanin cewa ana tafe da kudin da kuma motar da ke dauke da ita, wanda bayan hakan ne Buba Marwa ya bayar da umarnin a cafke kudin da kuma wanda ake zargi sannan a mika shi hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati domin cigaba da bincike.

A dayan bangaren, an kama wata mata mai jego mai suna Rashidat Adebayo a Offa da ke jihar Kwara dauke da miyagun magunguna da suka hada da Tramadol, Swinol, Diazepam da allurar Pentazocine.

Kara karanta wannan

Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata

Wannan na zuwa ne kasa da makonni uku bayan da jami'an hukumar NDLEA suka bada belin matar mai shekaru talatin da takwas bayan damke ta da miyagun kwayoyi.

Har ila yau, a jihar Adamawa, an cafke Sani Isa wanda aka fi sani da Bilaz da kuma Bala Yerima a Hong dauke da wiwi sunki 239 mai nauyin 209kg yayin dajami'an hukumar a Bauchi suka tare babbar mota da ke tahowa daga Legas zuwa Maiduguri a Azare, Bauchi.

An samu wiwi mai nauyin 164.8kg boye a kwalayen madar kuma duk aka jere su a babbar motar.

A yayin martani game da kamen, Marwa ya jinjinawa jami'an hukumar kan yadda suka kasance masu sanya ido da kuma hana kudin jabun shiga gari.

Ya kara da kira ga jami'an da ke Adamawa, Kwara, Bauchi da sauran jihohin da ke kasar da kada su yada makamansu wurin yaki da kwayoyi.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da kungiyar dillalan kwayoyi a Brazil, NDLEA

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce, babu ruwan ma'aikatan ta da sabgar hodar iblis mai nauyin kilogram 25 da ya hada da tawagar yan sanda karkashin jagoranci mataimakin kwamishinan 'yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari.

A wata takarda da kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a ranar Laraba, ya dora laifin a kan ma'aikatan hukumar 'yan sanda da kuma yadda wadanda ake zargin suka shirin shigo da haramtattun ababen daga Addis Ababa, Ethiopia.

'Yan sanda ne ke ikirari a wata takarda da suka fita ranar Litinin cewa, ma'aikatan NDLEA suna da sa hannu a harkallar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel