Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata

Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata

  • Wata kotun shari'ar Musulunci da ke zama a arewa maso gabas na Badakhashan a kasar Afghanistan ta sa anyi jifa kan wasu mace da namiji
  • Mace da namijin sun amsa laifi da ake zarginsu da shi a gaban kotu kan cewa har sau uku suna zina kuma an kawo shaidu adilai hudu
  • Kamar yadda mazauna yankin suka bayyana, an aiwatar da hukuncin jifansu har suka sheka lahira a bainar jama'a

An jefe wani mutum da wata mata a lardin arewa maso gabashin Badakhshan dake kasar Afghanistan, saboda sun aikata zina.

Ma'aikatan Taliban ne suka tabbatar da hakan a ranar Laraba. Wani ma'aikacin Taliban a lardin ya bayyana wa dpa yadda aka jefe su a kotun shari'a.

Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata
Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shari'ar musulunci ba ta yarda musulmai maza da mata su sadu da juna in ba da aure ba.

Kara karanta wannan

Ministar mata tayi kira ga maza da su dinga dukan matansu masu taurin kai, hakan ya janyo cece-kuce

Haka zalika, idan mijin aure yayi zina da matar aure, kuma aka samu shaidu hudu, za a jefe duka biyun.

"Da kansu sun amince da sun aikata zina, kuma sun yi hakan sau biyu zuwa uku," a cewar ma'aikacin.

Muezuddin Ahmadi, wanda ke kula da bangaren labarai da al'adun lardin ya ce, ana cigaba da bincikar lamarin, sannan ya yi alkawarin daukar tsatsauran mataki a kan wadanda suka jagoranci jifar.

Duk da bada tabbacin da hukumar tayi na cewa za ta girmama hakkin bil'adama, kananan ma'aikatan su da yawa suna karbar tsauraran horarwa a cikin watannin nan.

Karamar jaridar Hasht-e- Subh ta ruwaito yadda aka yi jifar a bainar jama'a a ranar Litinin a yankin Nasi dake lardin.

An samu labarin yadda kwamandan Taliban ya bada umarnin, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sake yi wa matafiya 'yan Kano da Nassarawa kisar gilla a hanyar Jos

Lamari irin wannan yayi kamari a fadin kasar tun lokacin da Taliban suka amshi mulki.

Ana hana dalibai mata da dama zuwa makarantar sakandare, kuma an hana mata da yawa koma wa bakin aikin su.

An tilasta mata su saka hijabi, sannan a hada su da muharramin su, idan za su yi tafiya mai nisa.

Ana bawa maza karfin gwuiwar tara gemu da sanya kayan gargajiya na Afghan, yayin zama a ofisoshin gwamnati, Vanguard ta rahoto hakan.

An haramta wake-wake a kafar sada zumuntar zamani. Wadanda suka gamu da irin takurawar, suna fuskantar hantara ko zaman gidan yari.

Matashi mai shekaru 19 ya dirka wa malamar shi mai shekaru 28 ciki, za ta haife shi

A wani labari na daban, Richard Nana Sam, dan kasar Ghana ne wanda ransa yayi matukar baci, sanadiyyar wani lamari dake wakana a gidan shi, wanda ya yanke shawarar fallasa wa a kafafan sada zumuntar zamani, da sa ran samun mafita.

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka

Yayin bada labarin kalubalen da yake fuskanta a wata sananniyar kungiyar 'yan Ghana dake da shafi a Facebook, ya kwashe labarin tun daga farko har karshe.

Richard ya bayyana yadda yayi wa yaran shi tagwaye (namiji da mace) masu shekaru 19 hayar malamar da za ta dunga koya musu karatu a gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel